Dama Ta Samu Yayin da Rundunar soji Ta Fara Daukar Sabbin Sojoji, Ta Fadi Yadda Za a Cike

Dama Ta Samu Yayin da Rundunar soji Ta Fara Daukar Sabbin Sojoji, Ta Fadi Yadda Za a Cike

  • Yayin da rashin tsaro ke kara kamari, rundunar sojin Najeriya ta na kokarin kara ma'aikata don dakile matsalar
  • Rundunar ta sanar da daukar sabbin sojoji a wannan shekara ta 2024 'yan gaba da sakandare (DSSC)
  • Ta ce an fara cike neman aikin ne daga jiya Alhamis 18 ga watan Janairu zuwa ranar Juma'a 23 ga watan Fabrairu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta sanar da diban sabbin sojoji wadanda za a dauka masu kwalin gaba da sakandare (DSSC).

Rundunar ta bayyana cewa dole masu sha'awar aikin sojan su cike bayanansu a yanar gizo kafin Juma'a 23 ga watan Faburairu.

Kara karanta wannan

Rundunar yan sanda ta dauki kasurgumin dan ta'adda, Bello Turji aiki? ACP Adejobi ya fayyace gaskiya

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da daukar sabbin sojoji
Rundunar sojin Najeriya za ta dauki sabbin sojoji. Hoto: Nigerian Army.
Asali: Twitter

Mene rundunar ke cewa kan daukar sojojin?

Legit ta leko cewa cika aikin kyauta ne kuma dama ce ga dukkan fararen hula da ma sojojin da suke aiki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a shafinta na X a yau Juma'a 19 ga watan Janairu.

Sanarwar ta ce:

"Dama ce ga fararen hula da kuma sojojin da suke aiki a Najeriya.
"Sojojin da rundunar ta dauki nauyinsu zuwa wasu hukumomi ne kadai za a ba su kulawa."

Karin bayani kan yadda za a cika aikin

Rundunar har ila yau, ta bada yadda za a cike aikin cikin sauki ba tare da wata matsala ba.

1. Ka shiga yanar gizo kamar haka recruitment.army.mil.ng sannan ka zabi bangaren DSSC.

2. Sannan za ka cike dukkan takardu da kuma bayanai da ake bukata kamar haka:

Kara karanta wannan

Matashi ya gurfana a kotu kan zargin taba muhibbar malamin addini a Kano

i. Fasfo

ii. Takardun makaranta

iii. Shaidar kasancewa a wata hukuma

iv. Shaidar kasancewa dan jiha

v. Takardar haihuwa

vi. Lambar NIN sa BVN

Sannan rundunar ta ce mafi karancin shekaru shi ne 20 yayin da 40 kuma shi ne karshe, cewar Daily Post.

'Yan bindiga sun kai hari gdajen sojoji

A wani labarin, Mahara sun farmaki gidajen sojoji a birnin Tarayya, Abuja da ke tsakiyar Najeriya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa yayin harin, maharan sun yi garkuwa da mutane biyu daga gidan.

Wannan na zuwa ne yayin da maharan suka addabi birnin Abuja musamman a 'yan kwanakin nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.