Dubi jiragen yaki na zamani da rundunar sojin sama ta baza domin ceto 'yan matan Dapchi
- Hukumar sojin sama ta baza karin wasu jiragen yaki na zamani domin zakulo inda 'yan matan Dapchi da ba a gani ba su ke
- Hukumar ta bukaci jama'ar dake garin Dapchi da Makwabtan su da su bayar da bayanai masu muhimmanci da kan iya taimakon jami'an ta
- Darektan hulda da jama'a na hukumar, Olatokunbo Adesanya, ya sanar da hakan a wata takardar sanarwa da ya sanyawa hannu
Hukumar sojin sama ta baza karin wasu jiragen yaki na zamani domin zakulo inda 'yan matan sakandiren 'yan mata ta Dapchi da ya zuwa yanzu ba a gani ba su ke.
A ranar litinin din makon jiya ne 'yan kungiyar Boko Haram su ka kai hari tare da yin awon gaba da wasu daga cikin daliban makarantar.
A jiya gwamnatin tarayya ta bakin ministan yada labarai kuma jagoran tawagar wakilcin gwamnatin tarayya ya sanar da cewar daliban makarantar sakandiren 110 ne ba a san inda suke ba har yanzu.
KARANTA WANNAN: Yadda sakacin sojoji ya jawo kai harin makarantar sakandiren 'yan mata dake Dapchi - Gwamna Gaidam
A jiyan ne kuma darektan hulda da jama'a na rundunar sojin sama, Olatokunbo Adesanya, ya sanar da cewar hukumar sojin sama ta kara yawan jiragen yaki masu dauke da na'urorin tsegumi a sararin samaniyar saman jihar Yobe domin zakulo inda 'yan matan 110 su ke.
Adesanya ya ce hukumar sojin sama tana gudanar da sintiri da atisaye a sararin samaniyar jihohin Borno da Yobe, illa iyaka ta kara yawan adadin jirage na musamman domin gaggauta zakulo inda 'yan matan su ke.
Kazalika sanarwar ta bukaci mazauna garin Dapchi da kauyukan kewayen garin da su samar da bayanai masu muhimmanci da kan iya taimakawa wajen gano inda daliban su ke.
Ga masu wani bayani mai muhimmanci, zasu iya tuntubar rundunar sojin sama a kan lambobin wayar hannu kamar haka; 08122557720, 08035733438, 08172843484 da 08058419128.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng