Lauya Mazaunin Kano Ya Magantu Kan Yadda Gwamna Abba Yusuf Zai Mayar Da Sanusi Kan Gadon Sarauta

Lauya Mazaunin Kano Ya Magantu Kan Yadda Gwamna Abba Yusuf Zai Mayar Da Sanusi Kan Gadon Sarauta

  • Wani lauya mazaunin Kano, Umar Sa'ad Hassan, ya ce ba boyayyen abu bane cewa Sanusi yana da kusanci da gwamnatin Gwamna Abba Yusuf
  • Umar ya ce dole sai gwamnatin Gwamna Yusuf ta samu wani laifi da za ta danganta da sarki na yanzu kafin ta iya dawo da Sanusi matsayin sarki
  • Yayin hira da Legit.ng ta yi da shi, ya ce shugaban jam'iyyar APC na kasa, na bukatar goyon bayan wasu manyan mutane daga NNPP kafin ya sake sake cin Kano

Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe

Jihar Kano - Wani kwararren mai sasanci, Umar Sa'ad Hassan, ya bayyana yadda gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta iya dawo da tubabben sarki, Sanusi Lamido Sanusi kan gadon sarauta.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya nuna gwamnan arewa 1, ya bayyana ayyukan Alherin da Yake Zuba Wa Talakawa

Umar ya ce abu daya kawai da ke hana Gwamna Yusuf mayar da Sanusi kan gadon sarautar Kano shine yadda hakan zai shafi siyasa.

Yadda Abba Gida-Gida zai iya mayar da Sanusi kan gadon sarautar Kano
Lauya mazaunin Kano ya ce zai fi sauki a mayar da Sanusi kan gadon sarauta idan an samu sarki na yanzu da laifi. Hoto: Sanusi Lamido Sanusi/Abba Yusuf
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin wata hira ta musamman da ya yi da Legit.ng, mazaunin Kano din ya ce babu wata gwamnati da za ta so ta lalata tsarin sarautar mutanen Kano musamman duba da cewa sarki na yanzu bai yi wani laifi ba.

Lauyan ya ce hanya mafi sauki da za a iya dawo da Sanusi a matsayin Sarkin Kano shine idan gwamnatin jihar Kano za ta iya gabatar da hujjar cewa ya yi laifi.

"Kusancin Sanusi da gwamnatin Abba Yusuf ba boyayyen abu bane. Abin da kawai na ke ganin suka hana shi shine batun siyasa. Babu wata gwamnatin da za ta so taba Sarauta musamman idan sarki na yanzu bai aikata wani laifi ba. Idan za su iya nuna wata laifi da sarkin na yanzu ya yi, abin zai zo da sauki.

Kara karanta wannan

Za a zauna: Kwankwaso ya aikawa Sarakunan Kano sako kwanaki da nasarar Kotun Koli

"Za su iya tursasawa mutane shi amma hakan ba zai yi dadi ba. Zai fi sauki idan za su iya danganta sarkin na yanzu da wani laifi."

Umar kuma ya yi magana kan yadda tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje zai farfado da siyarsa bayan Kotun Koli ta mayar da Gwamna Abba Yusuf kan kujerarsa.

Ya ce akwai yiwuwar Ganduje zai iya nasara a jihar saboda jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tana da mutane a jihar.

Lauyan ya ce akwai bukatar shugaban jam'iyyar na APC na kasa ya yi zawarcin wasu manyan yan siyasa daga jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) tare da goyon bayan wasu manyan yan jam'iyyarsa kafin ya samu nasara a jiharsa.

"Ba APC bane jam'iyyar da mutane Kano suka fi so a yanzu a Kano amma dai tana da mutane.
"Ya zama dole ya tara manyan jiga-jigan jam’iyyar da tare da farautar wasu manyan ‘yan siyasa a jam’iyyar NNPP kamar yadda Kwankwaso ya yi a lokacin da yake son yakar APC."

Kara karanta wannan

Ibadan: Adadin mutanen da suka mutu yayin da wani abu ya fashe a babban birnin jihar PDP ya ƙaru

Bidiyon Mahaifiyar Abba Ta Hadu Da Maman Sanusi, An Yi Batun Dawo da Sarki Sarautar Kano

A wani rahoton a baya, kun ji cewa mahaifiyar Gwamna Abba Kabir Yusuf ta kai ziyara wajen tsohuwar Mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II.

Wani bidiyo da Legit ta yi karo da shi a dandalin sada zumunta ya nuna Khadijatul-Naja'atu Yusuf tare da mahafiyar Khalifa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel