Hukuncin Kotun Koli: Yan Sanda Sun Kama Mutum 5 a Kano, Sun Tada Zaune Tsaye
- Kwamishinan 'yan sandan Kano ya ce rundunar ba za ta daga kafa ga duk wani magoyin bayan jam'iyyar siyasa da ya tada zaune tsaye a jihar ba
- Mr Gumel ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke sanar da cewa 'yan sandan jihar sun kama mutum biyar da laifin tayar da tarzoma a Gaya
- Rahotanni sun bayyana cewa an samu hatsaniya a tsakanin magoya bayan APC da NNPP bayan da Kotun Koli ta ba Abba Gida-Gida nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kano - Yan sanda a Kano sun ce sun kama mutum biyar daga suka tada zaune tsaye bayan da Kotun Koli ta yanke hukunci kan shari'ar zaben gwamnan Kano.
Kwamishinan 'yan sandan jihar, Malam Hussaini Gumel, ya bayyana hakan a wayar tarho da kamfanin dillancin labarin na kasa (NAN) a ranar Laraba.
An yi arangama tsakanin magoya bayan APC da NNPP
Gumel ya ce an samu hatsaniya tsakanin magoya bayan jam'iyyar NNPP da APC a karamar hukumar Gaya a yayin da ake gangamin murnar hukuncin kotun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jaridar Vanguard ta ruwaito kwamishinan yana cewa:
"Mun cafke mutum biyar zuwa yanzu, kuma mun kai mutum biyu asibiti da aka ji wa ciwo wajen gangamin."
Ya ce rundunar za ta gurfanar da wadanda ta kama gaban kotu da zaran ta kammala bincike.
Yan sanda sun gargadi 'yan siyasa kan tada zaune tsaye
Gumel ya gargadi 'yan siyasa a jihar da su kauracewa yin duk wani abu da zai iya kawo cikas ga zaman lafiya a jihar, Daily Post ta ruwaito.
Ya ce 'yan sanda da hadin guiwar sauran jami'an tsaro sun kara kaimi tare da tsaurara tsaro a wasu manyan wurare a jihar don dakile tashin tarzoma.
Ya ce:
"Ina kira ga 'yan siyasa da su guji saka magoya bayansu suna furta kalaman tunzurarwa, ko kuma haddasa fitina a cikin jihar Kano."
Kwamishinan ya ba da tabbacin cewa 'yan sanda za su samar da tsaro ga al'ummar jihar tare da bukatar kowa ya ci gaba da harkokinsa na yau da kullum ba tare da fargaba ba.
Doka ta haramta yin lefe a Kano, in ji Barista Hikima
Wani lauya a jihar Kano ya ce akwai wata doka da ta haramta yin kayan lefe, kayan daki, kayan na gani ina so da sauran tsarabe-tsaraben aure da ake yi a Kano.
A cewar Barista Abba Hikima, dokar ta tanadi hukuncin dauri ko biyan tara ko kuma a hada duka biyun ga wanda aka kama ya kai kayan lefe ko ya karba.
Asali: Legit.ng