Nasarawa: Fargaba Yayin da Matasan PDP Suka Aika Muhimmin Sako Ga Kotun Koli Gabannin Yanke Hukunci

Nasarawa: Fargaba Yayin da Matasan PDP Suka Aika Muhimmin Sako Ga Kotun Koli Gabannin Yanke Hukunci

  • Al'ummar Jihar Nasarawa sun kasa zaune sun kasa tsaye, sakamakon dakon hukuncin karshe da Kotun Kolin kasa za ta yanke
  • Kotun Kolin ta sanar da yau Talata, 16 ga watan Janairu 2024, a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan wanda ya halatta ya zama gwamnan jihar
  • Babbar jam'iyyar Adawa ta PDP a jihar, na fatan kotun ta jingine hukuncin kotun baya, biyo bayan nasarar da ta samu a kotun zabe

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Gabanannin hukuncin Kotun Koli kan zaben gwamnan jihar Nasarawa na ranar 18 ga watan Maris, matasan jam'iyyar adawa ta PDP sun aike da sako mai cike da gargadi.

Matasan nemi babbar kotun kasar da ta zamo a tsakiya ta hanyar tabbatar da gaskiya da kuma adalci, rahoton The Sun.

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar neman kifar da gwamnan Arewa, ta fadi dalilai

Kotun Koli za ta raba gardama a zaben gwamnan Nasarawa
Nasarawa: Fargaba Yayin da Matasan PDP Suka Aika Muhimmin Sako Ga Kotun Koli Gabannin Yanke Hukunci Hoto: David Ombugadu/Abdullahi Sule
Asali: Facebook

Da suke bayyana matsayar su a wani gangami da suka shirya a Keffi, jagoran kungiyar, Sani Mohammed, ya yabawa Shugaban kasa kasa Bola Tinubu kan janye hannunsa daga yiwa bangaren Shari'a katsalandan, rahoton Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun kuma yabawa babbar kotun kasar kan hukunce-hukuncen baya da ta yanke kan kujerun gwamnonin wasu jihohin kasar nan, wanda ya bayyana ƙarara cewa kotun ta tabbatar da bin bayan gaskiya.

Da yake jawabi kan hukuncin, Mohammed ya ce:

"Mun zo nan don yabawa shugaban kasarmu, Bola Ahmed Tinubu, kan kin sanya baki a harkokin shari'a, sannan abu na biyu muna kira ga dukkanin alkalan Kotun Koli da su yi adalci, musamman a batun Nasarawan nan.
"Ina gamsu sosai da hukuncin kotun koli zuwa yanzu, musamman a jihohin Kano da Filato. Ina mai yabawa Kotun Kolin kan wannan abu da ta yi, kuma ina so ta maimaita a jihar Nasarwa da izinin Allah."

Kara karanta wannan

Da an hana Abba Gida-Gida mulkin Kano, da Najeriya ta kama da wuta, inji Buba Galadima

Yadda APC ta ci banza a jihar Filato

A wani labarin, kotun daukaka kara ta tsige gwamnan jihar Filato, Caleb Mutfwang da duka ‘yan majalisan da aka zaba a karkashin PDP a bara.

Amma da aka je kotun koli, sai ga shi alkalai sun dawo da Mai girma Caleb Mutfwang a mulki, aka rusa hukucin da aka yi a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel