Betta Edu: Tinubu Zai Yi Garambawul a Kujerun Ministoci? Gaskiya Ta Fito

Betta Edu: Tinubu Zai Yi Garambawul a Kujerun Ministoci? Gaskiya Ta Fito

  • Gwamnatin Tarayya ta yi martani kan jita-jitar cewa za ta yi garambawul a mukaman ministoci da dama a kasar
  • An yi ta yada cewa Tinubu zai sauya wasu ministoci bayan zargin samun badakala a ma'aikatar jin kai da walwala
  • Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka yayin hira da gidan talabijin na NTA

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi martani kan jita-jitar cewa Shugaba Tinubu na shirin yin garambawul a kujerun Ministoci.

Ta ce wannan labarin ba shi da tushe bare makama inda ta bukaci mutane su yi watsi da shi, cewar Arise TV.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu ya warware abin da Ganduje ya so a shiryawa Kano a Kotun Koli Inji Abba

Fadar shugaban kasa ta yi martani kan jita-jitar yin garambawul a gwamnati
Tinubu ya musanta zargin garambawul a kujerun ministoci. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Mene Tinubu ke cewa kan zargin yin garambawul?

Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya bayyana haka yayin hira da gidan talabijin na NTA a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Wannan kirkirarren labari ne musamman idan har akwai alamar hakan zai iya faruwa.
"Amma ya na da muhimmanci kada mu rinka shigewa ayyukan shugaban kasa.
"Tinubu ya san duk abubuwan da suke faruwa kuma ya san masu yin aiki da wadanda ba su yi."

Ajuri ya ce shugaban ya na da hadima ta musamman a bangaren kula da ayyukan masu mukamai, Hadiza Bala Usman, cewar Vanguard.

Ya ce Tinubu ya na samum duk wasu bayanai dangane da kokarin da kowa ya ke yi a kujerarshi.

Ya kara da cewa idan akwai bukatar hakan ya kamata sai an kammala binciken zargin badakala a ma'aikatar jin kai da walwala tukun.

Kara karanta wannan

"Kada ku tsinewa shugabanninmu": Sarkin Musulmi ya aika muhimmin sako ga yan Najeriya

Har ila yau, Ngelale ya ce Tinubu ba zai taba barin wani ko wata da aka samu da badakalar kudade ko makamancin haka ba.

Rahotanni a baya sun ruwaito cewa akwai hasashen Tinubu zai yi garambawul bayan samun zargin badakalar makudan kudade a ma'aikatar jin kai da walwala a kasar.

Bala ya yabawa Tinubu kan halayensa

A wani labarin, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya yabawa Shugaba Tinubu kan bin doka a kasa.

Bala ya bayyana haka ne bayan samun nasara a Kotun Koli a ranar Juma'a 12 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel