Fansho da albashi: SERAP ta fitar da sunayen tsofin gwamnoni da ke cin 'tudu biyu' a asusun Najeriya
- 'Yan Najeriya sun fara shiga batun yaki da cin hanci domin taimakon kokarin gwamnati na kawo karshen matsalar
- Kungiyar SERAP ta fitar da jerin sunayen tsofin gwamnoni da ke karbar albashi a matsayin ministoci ko Sanatoci bayan kuma ana biyansu fansho
- SERAP, kungiya mai rajin yaki da cin hanci da tabbatar da adalci, ta kalubalantaci gwamnatin tarayya ta duba halaccin haka kamar yadda kotun tarayya ta bukata a shekarar 2019
A cikin martanin da ta mayar wa gwamnatin tarayya a kan batun tsofin gwamnonin da ke cin 'tudu biyu' daga asusun gwamnati, kungiyar SERAP ta saki jerin sunayen da gwamnatin tarayya ta nemi ta saki domin tabbatar da zargin da take yi.
A cikin takardar da mataimakin darekta a SERAP, Kolawole Oluwadare, ya fitar ranar Lahadi, SERAP ta lissafa jerin gwamnonin tare da yin kira ga ministan Shari'a, Abubakar Malami, a kan ya dauki mataki a kan tsofin gwamnonin.
Kungiyar ta bukaci Malami ya yi aiki da umarnin mai shari'a, Jastis Oluremi Oguntoyinbo, a kan gwamnati ta karbo dukkan fanshon da tsofofin gwamnonin suka karba yayin da suke rike da mukamin minista ko Sanata.
DUBA WANNAN: NCC ta bayyana dalilin sake rufe wasu layukan waya miliyan 2.2
Ga jerin sunayen tsofin gwamnonin kamar yadda SERAP ta fitar;
1. Rabiu Musa Kwankwaso (Kano)
2. Kabiru Gaya (Kano)
3. Godswill Akpabio
4. Theodore Orji (Abia)
5. Abdullahi Adamu (Nasarawa)
6. Sam Egwu (Ebonyi)
7. Shaaba Lafiagi (Kwara)
8. Joshua Dariye (Filato)
9. Jonah Jang (Filato)
10. Ahmed Sani Yarima (Zamfara)
11. Danjuma Goje (Gombe)
12. Bukar Abba Ibrahim (Yobe)
13. Adamu Aliero (Kebbi)
14. George Akume (Benuwe)
Oluwadare ya ce 'ya Najeriya suna jiran gwamnatin tarayya da ma'aikatar shari'a don ganin matakin da zasu dauka a kan tsofin gwamnonin.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng