‘Yan Siyasa da Sojojin da Aka Kashe a Juyin Mulkin Farko da Aka Yi a Junairun 1966
- A ranar 15 ga Junairu a shekarar 1966, sojoji suka fara hambarar da gwamnatin farar hula
- Juyin mulkin ne ya yi sanadiyyar mutuwar manyan yankin Arewa irinsu Ahmadu Bello
- Firayim Minista da wasu manyan sojojin Arewa sun hallaka a sanadiyyar juyin mulkin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - A ranar 15 ga watan Junairu a 1966, sojojin tawaye suka kifar da gwamnatin farar hula a karon farko a tarihin Najeriya.
Masana tarihi sun ce wannan bakin juyin-mulki ya jawo munanan abubuwan da suka biyo baya a kasar har zuwa yakin basasa.
Sojojin da suka hambarar da gwamnatin Abubakar Tafawa Balewa sun kashe mutane da yawa, rahoton nan ya jero su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Su wanene aka kashe a 1966?
1. Abubakar Tafawa Balewa
A juyin mulkin ne aka rasa Firimiyan Arewa, Abubakar Tafawa Balewa a Legas. Wanda ya jagoranci juyin mulkin, Emmanuel Ifeajuna ya kashe shi.
2. Ahmadu Bello
Manjo Chukuma Nzeogwu ya kashe Sardaunan Sokoto, Ahmadu Bello a gidansa a garin Kaduna tare da mai dakinsa, direbansa, dogari da kuma wani.
3. Samuel Akintola
Firimiyan Yamma a lokacin, Samuel Akintola ya ji labarin juyin mulkin kuma ya sanar da Ahmadu Bello. Akintola ya yi fada da sojoji kafin su harbe shi.
4. Festus Okotie-Eboh
Festus Okotie-Eboh yana cikin wadanda aka kashe daga kudancin Najeriya, ministan kudin mutumin Itsekiri da sojoji suka zarga da satar dukiyar kasa.
5. Birgediya Samuel Ademulegun
A juyin mulkin nan ne sojojin tawaye suka kashe Birgediya Samuel Ademulegun da mai dakinsa, Latifat, saura kiris ya gano shirin kifar da gwamnati a Kaduna.
6. Birgediya Zakariya Maimalari
Saura kiris Birgediya Zakariya Maimalari ya kubuta, sai ya ci karo da motar Ifeajuna wanda ya buda masa wuta, shi ne babban soja daga Arewa lokacin.
7. Kanal Kur Mohammed
Wani babban soja da ake ji da shi daga Arewa a lokacin shi ne Kanal Kur Mohammed. An yi garkuwa da sojan ne, daga baya sojojin suka buda masa wuta.
8. Kanal Ralph Shodeinde
Rahoton Nairaland ya ce babu tabbacin yadda Ralpha Shodeinde ya mutu. Laftanan Kanal din shi ne shugaban makarantar sojin NMTC da aka kashe shi.
9. Laftanan Kanal James Pam
Laftanan Kanal James Pam ya sanar da Janar Johnson Aguiyi-Ironsi da shirin juyin mulkin, shi ma har gida aka zo aka dauke shi, sai dai aka gano gawarsa.
10. Laftanan Kanal Arthur Unegbe
Chris Anuforo ya harbi Laftanan Kanal Arthur Unegbe, wasu sun ce an yi haka ne saboda gudun ya fallasa asirin
11. Laftanan Kanal Abogo Largema
An yi rashin dace Laftanan Kanal Abogo Largema ya baro birnin Ibadan, yana otel a Ikoyi a ranar, kamar Kur Muhammad da Maimalari, Largema Kanuri ne.
Sauran wadanda aka kashe su ne:
12. Ahmed Ben Musa
13. Hafsatu Bello
14. Mrs Latifat Ademulegun
15. Zarumi Sardauna
16. Ahmed Pategi
17. Sajen Daramola Oyegoke
18. PC Yohana Garkawa
19. Lans Kofir Musa Nimzo
20. PC Akpan Anduka
21. PC Hagai Lai
22. Philip Lewande
Zaben 2027 a Najeriya
Muddin ya gaza canza fasalin kasa da kirkiro da 'yan sanda a jihohi, Reno Omokri ya ce za a koma goyon bayan Atiku Abubakar.
An ji labari Omokri ya ce idan Peter Obi ya shiga takara a 2027, za a yi irin na 2023 da APC tayi nasara a karkashin Bola Tinubu.
Asali: Legit.ng