Menene dalilin da yasa aka kashe Ahmadu Bello Sardauna?
A yau an kwashe sama da shekaru 52 da suka gabata kenan da bindige gamji dan kwarai, Firimiya na farko kuma daya tilo na yankin Arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato.
Sir Ahmadu Bello ya kwanta dama ne a ranar Juma’a, 15 ga watan Janairu cikin watan Azumi na shekarar 1966, shekau shidda da samun yanci, inda wasu kananan hafsoshin soji suka far masa a daren juma’an suka yi masa ruwan harsasai.
KU KARANTA: Makarfi ya tsallake rijiya da baya a wani mummunan hatsarin mota
Manjo Chukwuemeka Kaduna Nzeogwu, wanda ya jagoranci kai harin ya bayyana dalilansa na kashe Sardauna; da suka hada da girman kai, cin hanci da rashawa, son kai, da kokarin kaddamar da jihadi a Najeriya.
Sai dai an tabbatar gaba daya wadannan dalilan daya dogara akansu duk shaci fadi ne, don kuwa ko bayan da aka kashe Sardauna, an tarar da Banki na binsa bashi ne ma, maganan son kai kuwa, ai a wancan lokaci kowane yankin kasar nan kokari take ta gina jama’anta da yankinta.
Wani na hannun daman Sardauna, Sheikh Abubakar Gumi ne da kansa ya fada ma Manjo Nzeogwu karya yake yi game da zargin Sardauna da yake na kokarin kaddamar da jihadi, inda Shehin Malamin ya fada masa Sardauna bai taba tara makamai a ko ina ba don shirin yaki.
Manya cikin wadanda aka hallaka a wannan rana, a cikin mutane 22, sun hada da Firai ministan Najeriya, Abubakar Tafawa Balewa, Firai ministan yankin yammacin kasar nan Samuel Akintola, janar Zakari Mai Malari, Ademulegun, Ahmad Ben Musa, Yakubu Pam, Largema, Kur Muhammad.
Ga jerin sunayen mutanen da aka hallaka nan:
Ahmadu Bello Sardauna
Abubakar Tafawa Balewa
Samuel Ladoke Akintola
Festus Okotie-Eboh ministan kudi
Shugaban hafsan Soji Birgediya Samuel Ademulegun da matarsa Latifat Ademulegun
Ahmed Ben Musa Maigadin Sardauna
Hafsatu Bello Uwargidar Sardauna
Zarumi, shima ma’aikaci a gidan Sardauna
Ahmed Pategi Direban Sardauna
Kanal Ralph Shodeinde
Birgediya Zakariya Maimalari
Kanal Kur Mohammed
Laftanar kanal Abogo Largema
Laftanar kanar James Pam
Sauran sun hada da:
Laftanar kanar Arthur Unegbe
Sajan Daramola Oyegoke abikin aikin Nzeogwu, daga baya Nzeogwun da kansa ya kashe shi
Yohana Garkawa
Kofur Musa Nimzo
Akpan Anduka
Hagai Lai
Philip lewande
Idan mai karatu ya duba jerin mutanen nan, zai fahimci dukkanin mutanen da aka kashe abokanan Sardauna ne a siyasance ko a addininance, ko kuma yanki daya ya hada su.
Yanzu karanta jerin mutanen da suka shirya tare da zartar da kashe wadannan bayin Allah da na ambata a sama:
Manjo Kaduna Nzeogwu
Manjo Adewale Ademoyega
Manjo Emmanuel Ifeajuna
Manjo Timothy Onwuatuegwu
Manjo Chris Anuforo
Manjo Humphrey Chukwuka
Manjo Don Okafor
Kyaftin Ogbo Oji
Sai mu kara tambayar kawunan mu, wai menene dalilin kashe Ahmadu Sardauna da Abubakar Tafawa Balewa?
Kalli dakin da Ojukwu ya boye a yayin yakin basasan Najeriya, kamar yadda Legit.ng ta kawo muku:
Asali: Legit.ng