Kano: Bayan Nasara a Kotu, Gwamnatin Kano Ta Magantu Kan Masu Niyyar Wawushe Asusun Jihar
- Gwamnatin jihar Kano ta ce ba za ta sassauta wa duk wanda aka kama da laifin cin hanci da rashawa da rashin da'a a jihar ba
- Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya bayyana hakan a taron tarbar Gwamna Abba bayan dawowarsa daga Abuja
- Gwarzo ya ce gwamantin Abba a jihar Kano za ta tabbatar da ta dawo da tattalin arzikin jihar tare da bunkasa ilimi, kiwon lafiya da sauran su
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Kano - Mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya ce gwamnatin jihar ba za ta kara amincewa da cin hanci da rashawa, wawure dukiyar al’umma, da rashin da’a a jihar ba.
Mataimakin gwamnan ya bayyana haka ne a wajen wani gangami na murnar dawowar gwamna Abba Kabir Yusuf Kano daga Abuja bayan nasarar da ya samu a Kotun Koli.
Kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito, Gwarzo ya yi jawabi ga mahalarta taron, inda ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Wasu marasa kunya sun yi yunkurin kalubalantar nufin Allah amma Allah Madaukakin Sarki ya ci ba su kunya, kuma a yau Gwamnan da aka zaba ya dawo."
Ya gargadi masu mugun nufi da su nisanta kansu daga muradun jama’a, yana mai jaddada kudirin gwamnati na yaki da zalunci da masu hadama.
Abin da gwamnatin Abba za ta yi a jihar Kano
Gwarzo ya jaddada cewa duk wanda baya goyon bayan cigaban Kano to ya nisanta kansa da gwamnatin jihar, kuma ya ce:
"Wannan gwamnati ta kudiri aniyar dawo da martabar tattalin arzikin jihar Kano, wanda ya fuskanci tabarbarewa daga masu son azurta kawunansu kawai.
"Mun hau mulkin Kano don yin aiki kuma za mu ci gaba da inganta abubuwan more rayuwa, tallafawa ilimi, jin daɗin jama'a, da samar da ingantattun cibiyoyin kiwon lafiya."
Gwarzo ya kara da cewa gwamnatin Abba na sane da hakkin jama’ar Kano da ke kanta, kuma za ta samar da damammaki ga matasa da mata.
Ya kuma yi kira ga al'ummar jihar musamman matasa da su kawo nesanta kansu daga ta’ammali da miyagun kwayoyi, satar waya da sauran laifuka.
Kotun Koli ta yanke hukunci kan shari'ar gwamnan Kano
A ranar Juma'a ne Kotun Koli ta yi zaman karshe kan shari'ar zaben gwamnan jihar Kano, inda ta tabbatar da cewa Abba Kabir Yusuf shi ne halastaccen gwamnan jihar.
A hukuncin da Kotun Kolin ta yanke, ta yi watsi da hukuncin da kotun kararrakin zabe da Kotun Daukaka Kara suka yanke na tsige Abba tare da ayyana Nasiru Gawuna matsayin wanda ya ci zaben.
Asali: Legit.ng