Barawon waya ya ci dukan tsiya a hannun fusatattun matasa, ya sheka barzahu

Barawon waya ya ci dukan tsiya a hannun fusatattun matasa, ya sheka barzahu

Miyagun ayyuka na karuwa a Najeriya, musamman a yanzu da gwamnatoci suka garkame jahohinsu don gudun yaduwar cutar Coronavirus, wanda hakan ya kawo zaman banza.

Fusatattun jama’a sun sauke fushinsu a kan wani matashi dan shekara 37 bayan ya yi ma wata mata kwacen wayar salular ta a karamar hukumar Warri ta kudu dake jahar Delta.

KU KARANTA: An sake samun bullar Coronavirus a Katsina, Masari ya garkame karamar hukumar Safana

Jaridar Punch ta ruwaito al’ummar yankin Kpoloko ne suka kama mutumin bayan ya kwace wayar matar a ranar Laraba, 23 ga watan Afrilu.

Ko da yake sun jibge shi son ransu, amma kwanansa bai kare ba har sai da suka mika shi zuwa hannun jami’an rundunar Yansandan Najeriya, reshen jahar Delta, inda ya mutu a caji ofis.

Wani shaidan gani da ido yace: “Jama’a sun diran masa ne tun kafin Yansanda su isa wurin, su biyu ne ma barayin, amma guda daya ya tsere. Yan fashi sun dade suna addabar yankin nan, ana kiransu Awala Boys.”

Barawon waya ya ci dukan tsiya a hannun fusatattun matasa, ya sheka barzahu

Wasu fusatattun matasa
Source: Twitter

Da majiyar mu ta tuntubi kakaakin rundunar Yansandan jahar, Onome Onovwakpoyeya game da lamarin, sai yace: “Eh da gaske ne, kafin Yansanda su isa wurin ya riga ya ci duka sosai, mun garzaya da shi zuwa asibiti, inda a can ya cika.”

A yanzu dai rundunar Yansandan jahar za ta cigaba da farautar abokin mamacin, wanda ya tsere yayin da jama’a suka fusata suka bi su domin damko wuyarsu.

A wani labari kuma, jami’an rundunar Yansandan jahar Legas sun samu nasarar kama wani kasurgumin dan fashi da makami daya fitini al’ummar yankin Ikorodu na jahar.

Yansanda sun kama Sanni Abiodun inkiya Abbey Boy ne a wani samame da suka kai wata matattarar yan wiwi dake unguwar Ikorodu ta jahar Legas.

Rahotanni sun ce an kama Abiodun ne a mashayar yan wiwin dake titin Araromi dake Igbogbo, inda Yansandan suka binciko wasu makamai tare da buhunan wiwi a wurin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel