An Kama Wani da Ake Zargi da Satar Solar a Masallaci a Kaduna, Ya Tona Asiri

An Kama Wani da Ake Zargi da Satar Solar a Masallaci a Kaduna, Ya Tona Asiri

  • Rundunar 'yan sanda ta cafke wani matashi kan zargin satar janareton masallacin Juma'a mai amfani da hasken rana
  • Rundunar ta ce ta yi nasarar kama matashin ne bayan rahoton jama'a a Hunkuyi da ke karamar hukumar Kudan a jihar
  • Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Mansir Hassan shi ya tabbatar da kame wani Basiru Rabiu kan zargin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kaduna - Rundunar 'yan sanda a jihar Kaduna ta cafke barawon janareton masallaci mai amfani da hasken rana.

An cafke matashin ne bayan satar janareton wanda ake amfani da shi a masallacin Juma'a da ke Hunkuyi a karamar hukumar Kudan a jihar.

Kara karanta wannan

Kano: Mota ta murkushe mai kwacen waya jim kadan bayan fauce wayar wata, ya shiga kakani-kayi

'Yan sanda sun cafke wani matashi kan zargin satar janareton masallacin Juma'a
Rundunar ta yi nasarar cafke matashin ne bayan samun rahoto. Hoto: NPF.
Asali: Twitter

Mene rundunar 'yan sandan ke cewa a Kaduna?

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Mansir Hassan shi ya tabbatar da kame wani Basiru Rabiu kan zargin, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mansir ya ce rundunar ta yi nasarar cafke matashin ne bayan mutane su na zargin shi a kusa da masallacin.

Bayan cafke matashin, ya tabbatar da cewa shi ya sace janareton da ke amfani da hasken rana a masallacin Juma'ar.

Meye martanin matashin da ake zargin ga 'yan sanda?

Wanda ake zargin ya kuma tabbatar da sace irin wannan kayan a kauyen Nahuce inda ya siyar da su ga wani mai suna Mansir Umar.

Kakakin rundunar har ila yau ya ce an cafke wanda ya sayi kayan kuma yanzu haka ana kan bincike, cewar Vanguard.

Yawan satar kayayyakin masallaci da ake ibada kullum karuwa ya ke yi musamman a jihohin Arewa da Musulmai su ka fi yawa.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama wani hatsabibin shugaban 'yan bindiga a kasuwar jihar Arewa

Mota ta murkushe matashi bayan kwacen waya a Kano

A wani labarin, rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta tabbatar da cewa mota ta buge wani matashi jim kadan bayan ya kwace wayar wata mata.

Matashin ya gamu da tsautsayin ne bayan ya yi fashin wayar yayin tsallaka titi a Zoo Road da ke birnin Kano.

An dauki matashin zuwa asibiti don ba shi kulawar gaggawa amma ya samu raunuka da dama a jikinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.