Kyawawan halayen manzon Allah ﷺ : Labarinshi da wani mashayi

Kyawawan halayen manzon Allah ﷺ : Labarinshi da wani mashayi

A zamanin manzon Allah akwai wani mutum mai suna Abdullah wanda ke son Allah da manzonsa sosai.

Saboda soyayyan da yakewa manzon Allah, yana kawo ma manzon Allah duk abu mai kyau da ya shigo Madina, idan wani yazo da zuma ko wani abu, zai dauka ya bawa manzon Allah ﷺ.

Amma daga baya, idan mai kayan ya tambayeshi kudi, sai Abdullah ya kawo shi wajen manzon Allah sai yace : “ Ka bashi kudin kayansa,”

Sai manzon Allah yace:

“ Shin ba kyauta ka bani ba?

Sai Abdullah yace: “ Hakane manzon Allah ; amma na kasa biya.”

Sai manzon Allah ya kwashe da dariya da Abdullah, sai manzon Allah ya biya kudin.

Amma matsalan shine Abdullah mashayi ne. sai ya bugu za’a kawoshi wajen manzon Allah cikin maye domin ayi masa haddi. Sai ayi masa.

An kasance ana masa hakan koda yaushe.

Bayan an gama masa haddi wata ranan, lokacin da Abdullah ya tafi, sai wani sahabi yace : “ Allah ya tsine mai! Sau nawa za’a dinga masa haddi”

Sai manzon Allah yace: “ Kada ka tsine masa, Baka san son da yakewa Allah da manzon Allah.” Bukhari.

Sannan ya kara cewa : “ Kada ka taimaka wa shaidan akan dan uwanku.”

https://twitter.com/naijcomhausa

https://web.facebook.com/naijcomhausa/#

Asali: Legit.ng

Online view pixel