Yanzu-yanzu: An kai hari majalisar dokokin Ogun, an yi awon gaba da sandar majalisa

Yanzu-yanzu: An kai hari majalisar dokokin Ogun, an yi awon gaba da sandar majalisa

- Barayi sun fasa cikin majalisar dokokin jihar Ogun ranar Alhamis

- Kakakin majalisan ya ce satan bai da wani alaka da siyasa saboda babu wani matsala tsakanin mambobin majalisar

- Ya gayyaci yan sanda somin gudanar da bincike kan lamarin

Wasu yan baranda a ranar Alhamis sun kai hari majalisar dokokin jihar Ogun kuma sun yi awon gaba da sandar iko na majalisar.

Channels TV ta ce Kakakin hukumar yan sandan jihar, Abimbola Oyeyemi, ya tabbatar da labarin.

Ya ce matasan sun fasa cikin majalisan ne da safiyar Alhamis kuma suka dauke sandar.

Ya ce amma an samu kwato kan sanda dake dauke da tambarin Najeriya, har yanzu ana neman sauran jikin.

An kaddamar da bincike kan wadanda suka aikata hakan da wanda ya turo su, ya kara.

KU KARANTA: Zanga-zanga ya barke a Fatakwal bayan dan sanda ya bindige direban Keke-Napep kan N100 (Bidiyo)

Yanzu-yanzu: An kai hari majalisar dokokin Ogun, an yi awon gaba da sandar majalia
Yanzu-yanzu: An kai hari majalisar dokokin Ogun, an yi awon gaba da sandar majalia
Source: Original

Kakakin majalisar, Olakunle Oluomo, ya tabbatar da aukuwan hakan amma ya ce sace sandar ikon bai da alaka da siyasa.

A hirar da yayi da Channels, ya bayyana cewa barayi ne kawai kuma ta cikin kwanon rufin majalisar suka shigo.

Kalli bidiyon hirarsa:

KU DUBA: Najeriya fa kamar mota ce mara direba, Wole Soyinka

A bangare guda, ana zargin cewa wasu barayi sun shiga gidan gwamnatin jihar Akwa Ibom, sun kuma yi awon gaba da wasu kudi da ba a san adadinsu ba.

Daily Trust ta ce an ware wannan kudi ne da sun kai miliyoyin Naira domin a biya ‘yan jarida.

Jaridar tace an kutsa cikin ofishin babban sakataren yada labaran gwamnan Akwa Ibom, Ekerette Udoh, inda aka ajiye wannan kudi, aka sace su.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel