Malamin Jami'ar Abuja Ya Tsere Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane

Malamin Jami'ar Abuja Ya Tsere Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane

  • Malamin Jami'ar Veritas da masu garkuwa suka sace a Otukpo, Jihar Benue ya shaki iskar yanci
  • Evelyn Obekpa, mai magana da yawun jami'ar Veritas ta tabbatar da sakin Dr John Adole bayan yan bindigan sun sace shi
  • Okekpa ta kara da cewa ba a biya kudin fansa ba tana mai cewa Dr Adole tsere wa ya yi daga hannun masu garkuwan da suka kama shi

The Punch ta rahoto cewa Shugaban tsangayar Tarihi da Nazarin Harkokin Kasa da Kasa a Jami'ar Veritas a Abuja, Dr John Adole, ya shaki iskar yanci.

Wasu yan bindiga ne suka sace Adole a Otukpo, a karamar hukumar Otukpo na Jihar Benue a ranar Lahadi.

Malamin Jami'ar Abuja Ya Tsere Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane
Malamin Jami'a Da Yan Bindiga Suka Sace Ya Tsere. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

Wasu mutane uku, ciki har da wani Farfesa daga Jami'ar Jihar Benue, Makurdi sun tsallake rijiya da baya yayin da yan bindigan suka kai harin, LIB ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

An tattaro cewa malamin jami'ar ya tsere daga hannun wadanda suka sace shi a ranar Litinin.

Jami'ar Veritas ta tabbatar da sakin Dr John Adole

Mai magana da yawun jami'ar Veritas, Evelyn Obekpa, ta tabbatar da hakan ga wakilin majiyar Legit.ng a ranar Talata.

Ta ce:

"Dr John Adole, Shugaban tsangayar Tarihi da Nazarin Harkokin Kasa da Kasa a Jami'ar Veritas a Abuja, wanda yan bindiga suka sace a Otukpo, Jihar Benue, a ranar Lahadi, 1 ga watan Mayun 2022, ya tsere daga hannun masu garkuwar.
"Shugaban Jami'ar Veritas da ke Abuja, ya yi magana da Dr Adole da matarsa a yammacin ranar Litinin."

Da aka tambaya ko an biya kudin fansa kafin sakinsa, ta bada amsa da cewa:

"Ya tsere ne."

'Yan Sanda Sun Cafke Matashin Da Ke Kai Wa 'Yan Bindigan Neja Abinci

Kara karanta wannan

'Batanci: Jakadiyar Birtaniya Ta Ce Dole a Hukunta Waɗanda Suka Kashe Ɗalibar Sokoto

A wani rahoton, Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta kama wani matashi mai shekaru 20, Umar Dauda wanda ake zargin yana kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a jihar, The Punch ta ruwaito.

A wata takarda wacce jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya sanya wa hannu, an samu bayani akan yadda aka kama matashin bayan mazauna yankin sun bayar da bayanan sirri ga hukuma.

Kamar yadda takardar tazo:

“An yi kamen ne a ranar 16 ga watan Maris din 2022, da misalin karfe 11 na dare bayan samun bayanan sirri akan yadda ake yawan ganin wani mai kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a kauyen Kapako da ke Lapai.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164