Yadda Wani Mutum Sanye Da Kayan Mata Dauke Da Goyo Ya Bayyana A Wani Bidiyo

Yadda Wani Mutum Sanye Da Kayan Mata Dauke Da Goyo Ya Bayyana A Wani Bidiyo

  • Wani matashi ya biyo wani layi dauke da goyo a bayansa, bidiyon ya girgiza kafar sadarwar Tik-Tok
  • A bidiyon an ga mutumin dauke da jakar mata ta hannu, da kuma dan kunne yana tafiya kamar wata uwa
  • A maganar da ake yanzu bidiyon ya samu sama da mutum miliyan guda da suka kalla da kuma sharhi daga wanda suka kalla din

Masu amfani da kafar Tik-Tok sunyi nishadi gami da dariya game da wani mutum wadda ya biyo wani layi dauke da goyan yariya a bayansa.

Bidiyon wanda baida tsayi, kuma @papaskits ya wallafa, an ga wani mutum dauke da kayan mata, takalmi mai tudu da kuma dan kunne suna lilo a kunnensa

Bidiyon mai tsawon dakika 14 an ga wani layi da mutane ke hidin-dimusunsu ba tare da da wata fargaba ko matsala ba, kowa na sabgar gabansa.

Kara karanta wannan

Yan Najeriya Sun Zagaye Mai Kama Da Shugaba Buhari a Wani Bidiyo Da Ya Yadu

Mutumin dauke da goyo da kuma wata yarinya ya goya ta ya yadu, an ga mutumin sanye da kayan mata kuma yana tafe kamar wata uwa kuma yana tauna cingam.

Ana tunanin bidiyon an daukeshi ne lokacin bukuwan karshe/farkon shekara sabida an ganshi sanye da hular Fada Xmas.

Masu amfani da Tik-Tik sunyi shari, sunyi dariya, sunyi maganganu, sannan kuma ya samu wanda suka kalla kusan mutum miliyan daya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sharhin masu amfani da Tik-Tok

@Shaun Makola Mankind yace:

"Naji dadin yadda kowa yai watsi da shi, mun fara ci gaba a al'ummar"

@Sinazo yayi sharhi:

"Ko a jikina wai an harbi karsana"

@user8531316825908 yace:

"wannan yarinyar mai jan kaya itace kadai mai rai a garin nan"

@OLGa reacted:

"naji dadi yadda kowa yayi banza bai kula shi ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel