Ana Saura Awanni Kadan a Yanke Hukunci, PDP a Jihar Arewa Ta Mika Lamarinta Ga Allah, Ta Yi Gargadi

Ana Saura Awanni Kadan a Yanke Hukunci, PDP a Jihar Arewa Ta Mika Lamarinta Ga Allah, Ta Yi Gargadi

  • Jam'iyya PDP ta bukaci magoya bayanta su koma ga Ubangiji yayin da ake shirin yanke hukuncin karshe a zaben Plateau
  • Jamiyyar ta bukaci dukkan mambobinta da su dage da addu'o'i da kuma tashi da azumi don neman nasara
  • Legit Hausa ta ji ta bakin wani dan jam'iyyar PDP a Jos kan wannan wannan shari'ar da ake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Plateau - Yayin da ake shirin yanke hukuncin zaben jihar Plateau, magoyan bayan PDP sun koma ga Allah.

Magoya bayan sun dauki matakin ne don neman nasara a Kotun Koli a shari'ar da za a karkare gobe Juma'a 12 ga watan Janairu.

Kara karanta wannan

Fitaccen dan Majalisa ya shiga takarar neman gwamna a jihar PDP, ya caccaki gwamna mai ci

PDP ta koma ga Ubangiji yayin da ake daf da yanke hukuncin zabe
PDP ta bukaci magoya bayanta su tashi da azumi. Hoto: Caleb Mutfwang, Nentawe Goshwe.
Asali: UGC

Wane umarni shugabannin PDP suka bayar?

Shugaban jam'iyyar PDP a jihar, Hon. Chris Hassan ya bukaci dukkan magoya bayansu su yi addu'a da kuma daukar azumi, cewar Leadership.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hassan a cikin wata sanarwa da ya fitar a Jos dauke da sa hannun hadiminsa, Kefas Sumdi ya ce su na da kwarin gwiwa.

Sanarwar ta ce:

"Addu'o'i da azumi ya zama dole a yanzu don neman nasara a Kotun Koli.
"Mu na fatan ubangiji ya taimake mu a shari'ar d ake yi ya tabbatar da Gwamna Caleb Mutfwang a matsayin gwamnan jihar."

Wane gargadi kuma jami'yyar PDP ta yi?

Hon. Hassan har ila yau, ya bukaci magoya bayan jam'iyyar su kwantar da hankulansu ba tare da wata tarzoma ba.

Ya ce kada su tsorata duk abin da aka fauwala wa Ubangiji zai iya komai fiye da tunaninsu, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Betta Edu: Gwamonin APC sun dauki mataki ana tsaka da binciken badakala, bayanai sun fito

Legit Hausa ta ji ta bakin wani dan jam'iyyar PDP a Jos kan wannan lamari:

Muhammad Sani Jos ya ce tabbas sai an hada da addu'a domin komai idan aka saka Allah akwai nasara a ciki.

Da wakilin Legit Hausa ya tambaye shi ko su na da kwarin gwiwa a kan shari'ar, sai ya ce:

"Tabbas mu na jin a jikinmu akwai kwarin gwiwa duk da kwace sauran kujerun 'yan Majalisa da aka yi."

An sanar da ranar yanke hukunci a Plateau

A wani labarin, Kotun Koli ta sanya Juma'a 12 ga watan Janairu a matsayin ranar yanke hukunci a zaben Plateau.

Gwamna Caleb Mutfwang ne ya kalubalanci hukuncin Kotun Daukaka Kara bayan ta rusa zaben shi a watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.