Ciki Ya Duri Ruwa Yayin da Ake Saura Awanni Kadan a Yanke Hukunci a Kano da Zamfara da Jihohi 6

Ciki Ya Duri Ruwa Yayin da Ake Saura Awanni Kadan a Yanke Hukunci a Kano da Zamfara da Jihohi 6

  • Ana ci gaba da zaman dar-dar a Kano yayin da yau ake dakon hukuncin karshe a shari’ar zaben jihar
  • A yau Juma’a ce 12 ga watan Janairu Kotun Koli za ta raba gardama a jihohi takwas da ake shirin yanke hukunci
  • Jihohin sun hada da Kano da Zamfara da Plateau da Legas da Bauchi da Cross River da Abia da kuma Ebonyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano – Yayin da ake zaman dar-dar a jihohin Kano da Zamfara da Plateau da sauransu, an tsaurara tsaro.

A yau Juma’a ce 12 ga watan Janairu Kotun Koli za ta raba gardama a jihohi takwas da ake shirin yanke hukuncin karshe.

Kara karanta wannan

Yusuf vs Gawuna: Sabon hasashe ya nuna wanda zai yi nasara a Kotun Koli a shari'ar Kano

Ana daf da yanke hukuncin Kano da Zamfara da sauran jihohi 6
A yau Juma'a ce za a yanke hukuncin karshe a jihohin. Hoto: Caleb Mutfwang, Abba Kabir, Dauda Lawal.
Asali: Facebook

Wasu jihohi ne za a yanke hukuncin?

Jihohin sun hada da Kano da Zamfara da Plateau da Legas da Bauchi da Cross River da Abia da kuma Ebonyi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jihar Kano wacce ita ce shari’ar da tafi daukar hankulan ‘yan Najeriya gaba daya, Daily Trust ta tattaro cewa ana ta zaman dar-dar da cece-kuce kan shari’ar.

Yayin da ake cikin wannan hali, Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Hussaini Gumel ya ce sun shirya tsaf don dakin tashin-tashina a jihar.

Gumel ya ce sun baza jami’an tsaro a wurare na musamman a Kano inda ya gargadi masu son tada kayar baya, cewar Leadership.

Wane tanadi 'yan sanda su ka yi?

Da aka tambaye shi ko za a iya sanya dokar ta baci, sai ya ce ba dole ba ne amma dai za su dakile duk wasu masu son ta da hankali.

Kara karanta wannan

Ana saura awanni kadan a yanke hukunci, PDP a jihar Arewa ta mika lamarinta ga Allah, ta yi gargadi

Shugaban jam’iyyar NNPP a jihar, Hashimu Dogonruwa ya ce su na da tabbacin wannan nasara ta su ce da yardar Allah.

A bangarenshi, sakataren yada labaran APC a jihar, Ahmad Aruwa ya ce da yardar Allah nasara ta APC ce ganin yadda suka mika shaidu masu karfi.

A Plateau da Zamfara kuwa, jami'an ‘yan sanda a jihohin sun tabbatar da wadatar jami’an tsaro don kawo zaman lafiya a jihohin.

Haka a jihohin Legas da Bauchi, dukkan shirye-shirye sun kankama don tabbatar da zaman lafiya bayan yanke hukuncin.

PDP ta koma ga Allah a Plateau

Kun ji cewa, jam'iyyar PDP a jihar Plateau ta mika lamuranta ga ubangiji yayin da ake shirin yanke hukunci.

Jam'iyyar ta bukaci magiya bayanta su tashi da azumi da kuma addu'o'i don neman nasara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel