Betta Edu: An Bayyana Abu 1 da Ya Kamata Yan Najeriya Su Yi Wa Dakatacciyar Ministar Tinubu
- Tsohon mataimakin gwamnan jihar Legas ya yi kira ga ƴan Najeriya da su sake ba Betta Edu dama a karo na biyu
- Femi Pedro ya yi wannan kiran ne bayan shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da ministar daga kan muƙaminta
- Pedro ya yi nuni da cewa halin da ministar ta tsinci kanta a yanzu zai sanya ta gyara kura-kuran da ta yi a nan gaba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Femi Pedro, tsohon mataimakin gwamnan jihar Legas, ya roki ƴan Najeriya da su sake baBetta Edu, ministar ayyukan jin ƙai da yaƙi da talauci da aka dakatar, dama a karo na biyu.
Tsohon mataimakin gwamnan na jihar Legas a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ya ce za ta koyi darasi mai zurfi daga kura-kuran da ta yi, sannan ta yi abin da ya dace nan gaba, cewar rahoton jaridar TheCable.
Wannan kiran na sa dai na zuwa ne bayan shugaban ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da ita kan badaƙalar N586m.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dakatar da ita kuma ke da wuya hukumar EFCC, ta duƙufa bincike a kanta kan yadda kuɗaɗen ma'aikatar suka yi ɓatan dabo.
Wane kira Pedro ya yi?
A kalamansa:
"Dukkanmu mun karanta irin laifukan da ta aikata da kuma dakatarwar da shugaban ƙasa ya yi mata da kuma tambayoyin da EFCC ta yi mata
"Wannan shi ne yadda ya kamata. Ina fata da addu'a cewa a ƙarshe, za ta koyi darasi mai zurfi a kan yadda za ta gudanar da kanta a matsayin jami'ar gwamnati da sanin yadda ake gudanar da lamura."
Jaridar Leadership ta ce Pedro ya shawarci matasan Najeriya da aka nada a ma’aikatun gwamnati, da su samu waɗanda za su riƙa ba su shawara kan yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati.
Ya ƙara da cewa:
"Al'ummar ƙasar nan na buƙatar ƙarin matasa a aikin gwamnati kuma ina fatan abin da ya faru da ita ba zai karya gwiwoyin masu shekaru irin na ta ba."
Rigimar Halima da Betta Edu
A baya labari ya zo kan dalilin da ya haddasa rigima a tsakanin Betta Edu da dakatacciyar shugabar hukumar NSIPA, Halima Shehu.
Rahotanni sun yi nuni da cewa matsalar kuɗi ce ta auku a tsakaninsu inda har ta kai ga rashin jituwa a tsakaninsu.
Asali: Legit.ng