Tinubu Ya Lalubo Tsohon Hadimin Atiku da Ya ‘Fasa Kwai', Ya Ba Shi Mukamin Gwamnati

Tinubu Ya Lalubo Tsohon Hadimin Atiku da Ya ‘Fasa Kwai', Ya Ba Shi Mukamin Gwamnati

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada sababbin darektoci a ma’aikata harkokin jiragen sama a Najeriya
  • Michael Achimugu wanda ya yi aiki da Atiku Abubakar a shekarun baya, yana cikin wadanda aka ba mukamai
  • Kafin zaben 2023, Achimugu ya yi wa Atiku illa da ya zargi ‘dan takaran shugaban kasar na PDP da cin amanar kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya amince da nadin Michael Achimugu a matsayin sabon Darekta a hukumar NCAA ta kasa.

Shugaban Najeriyan ya nada Mista Michael Achimugu ne bayan gwamnatin tarayya ta kori Darektoci a ma’aikatar harkokinjiragen sama.

Tinubu, Atiku
Bola Tinubu, Micheal Achimugu da Atiku Abubakar Hoto: @Dolusegun16, Atiku da michael-achimugu
Asali: Facebook

Micheal Achimugu da Atiku Abubakar

Premium Times ta tunawa jama’a cewa sabon Darektan na NCAA ya taba aiki da Atiku Abubakar mai takarar shugaban kasa a PDP.

Kara karanta wannan

Kotun Koli na shirin yanke hukunci kan zaben Kano, Shugaba Tinubu ya aike da muhimmin saƙo ga Ganduje

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin da ake shirin zaben 2023, Achimugu ya fito ya zargi tsohon ubangidansa da rashin gaskiya, hakan ya bata ‘dan takaran adawan.

Tsohon mukarrabin ya jefi Atiku Abubakar da yin ba daidai da domin samun yadda yake so a lokacin yana mataimakin shugaban kasa.

Achimugu ya samu mukami a mulkin Tinubu

A yanzu, Achimugu ya zama Darektan hulda da jama’a da kare abokan kasuwanci a NCAA mai kulda da harkokin dokokin jiragen sama.

Achimugu da wasu sababbin Darektoci biyar Festus Keyamo ya nada su canji wadanda Hadi Sirika ya kawo kafin ya bar ofis a Mayu.

Meyasa Achimugu ya juyawa Atiku baya?

A hira da aka yi da Mr Achimugu gabanin zabe, ya jefi Atiku Abubakar da yin amfani da SPV domin satar dukiyar al’umma a gwamnati.

Kara karanta wannan

Shugaba Bola Tinubu ya dira jihar Legas, an bayyana muhimmin abinda zai yi

Kamar yadda ya fada, ya fallasa tsohon mai gidansa ne saboda ya wayar da kan ‘yan Najeriya domin su guji zabensa ya zama shugaba.

Alakar Keyamo da Achimugu

Bayan hirar aka ji Festus Keyamo a lokacin yana kakakin kwamitin kamfen APC, ya fito yana kiran jami’an tsaro su cafke Atiku Abubakar.

Da Keyamo SAN ya zama Minista, ya jawo wannan mutumi har ya ba shi mukami.

Martanin Godwin Emefiele

A daren yau aka samu labari Godwin Emefiele ya wanke kan shi daga zargin satar kudi da wasu laifuffuka da yake gwamnan bankin CBN.

Emefiele ya ce batun canza Nairori da cire $6.23m daga asusun CBN ba duk gaskiya ba ne, kuma ya nuna zai kotu saboda an yi masa sharri.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng