Bankin Musulunci Zai Daga Darajar Kano, Zai Yi Wani Aikin Naira Biliyan 4, an Samu Karin Bayani

Bankin Musulunci Zai Daga Darajar Kano, Zai Yi Wani Aikin Naira Biliyan 4, an Samu Karin Bayani

  • Bankin IsDB da asusun LLF karkashin shirin KSADP za su gina manyan cibiyoyin tara madara guda 60 a fadin jihar Kano
  • A cewar kodinetan shirin KSADP, cibiyoyin za su cike gibin da ke tsakanin makiyaya da masana’antar sarrafa madara
  • Wannan aikin samar da cibiyoyin zai lakume naira biliyan hudu, kuma za a dauki tsawon watanni ana yin sa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Shirin bunkasa noma da makiyaya ta jihar Kano (KSADP) ya bayar da kwangilar aikin gina cibiyoyin tara madara guda 60 a fadin jihar Kano.

Bankin cigaban Musulunci (IsDB) da kuma asusun inganta rayuwa (LLF) ne ke daukar nauyin dukkan ayyukan shirin na KSADP.

Kara karanta wannan

Betta Edu: EFCC ta bugi ruwan cikin manyan jami’ai 10 na ma’aikatar jin kai, bayanai sun fito

Za a gidan cibiyoyin tara madarar shanu a Kano.
IsDB da LLF za su kashe naira biliyan 4 don gina cibiyoyin tara madarar shanu a Kano. HOTO: Getty Images
Asali: Getty Images

Shirin KSADP ta bakin Ameen K Yassar ya ce an bayar da kwangilar ne a rukunai hudu ga wasu kamfanoni hudu tare da hasashen kammala kowanne rukuni a watanni 12.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manufar samar da cibiyoyin tatsa da tara madara a Kano

Daily Trust ta ruwaito cewa, kowace cibiyar tara madara za a saka mata rijiyar burtsatsemai amfani da hasken rana da tankin ruwa mai cin lita 20,000; da dai sauran kayan aiki.

Bugu da kari, kowacce cibiya za ta sami tanki mai lita 250 mai hade da na'urar sanyi da kuma na'urar gwajin madara tare da samar da gwangwanayen tara madarar.

Kodinetan shirin KSAPDP, Ibrahim Garba Muhammad ya ce babu irin wannan ciyar a Najeriya kuma za ta cike gibin da ke tsakanin makiyaya da masana’antar sarrafa madara, rahoton Premium Times.

Kara karanta wannan

Aikin Allah: Hisbah ta dauki mataki bayan kama kwalaben giya a Katsina

Kotu ta garkame matashin da ya kashe limami a Kano

A wani labarin daga jihar Kano, wata kotun Majistire ta ba da umurnin kulle matashin da ya kashe limami saboda ya hana su shan wiwi a kusa da masallaci a unguwar Jakara da ke birnin Kano.

A ranar 31 ga watan Disamba 2023 ne aka ruwaito matashin mai suna Yusuf Haruna ya kashe Liman Sani Mohammed ta hanyar daba masa wuka a baya.

Kotun ta kuma garkame mahaifin Yusuf saboda zargin sa da yaron nasa mafaka bayan da ya aikata kisan kan, inda ta dage zaman kotun zuwa ranar 31 ga watan Janairu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.