Babban Labari: Hukumar EFCC Ta Karbe Fasfon Betta Edu da Sadiya Umar-Farouq

Babban Labari: Hukumar EFCC Ta Karbe Fasfon Betta Edu da Sadiya Umar-Farouq

  • Betta Edu ta shafe awanni ta na amsa tambayoyi daga jami’an EFCC masu yaki da rashin gaskiya
  • Ministar kasar da aka dakatar ta mika kan ta ga hukuma domin a binciki zargin da ake yi mata
  • Majiya ta ce EFCC ta raba Edu da Sadiya Umar-Farouq da fasfonsu domin a hana su tserewa

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya ta karbe fasfon Ministar jin kai da shugaban kasa ya dakatar watau Betta Edu.

Haka zalika Punch ta ce an karbe takardun fasfon Hajiya Sadiya Umar-Farouq wanda ta rike wannan kujera tsakanin 2019 da 2023.

Betta Edu
Betta Edu da Sadiya Umar-Farouq Hoto: @Edu_Betta, @Sadiya.Farouk
Asali: Twitter

Dr. Betta Edu ta ziyarci hedikwatarta EFCC a Abuja ne da kimanin karfe 10:00 na safiyar Talata domin amsa tambayoyi daga jami’ai.

Kara karanta wannan

Ministar da aka dakatar, Betta Edu ta shiga hannun hukumar EFCC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har zuwa karfe 7:00 na yamma, an tabbatar da Betta Edu ta na hannun hukumar EFCC.

An karbe fasfon Sadiyar Umar-Farouq

Dakataciyyar ministar ba ta bada wani uzuri kamar yadda Sadiyar Umar-Farouq ta yi a makon jiya ba, nan ta ke ta mika kan ta ga hukuma.

Rahoton ya ce an yi kusan awanni 12 ana yi wa Sadiyar Umar-Farouq a kan zargin wasu N37.1bn da aka karkatar a lokacin da ta ke ofis.

Kafin a bada belin tsohuwar ministar, sai da aka tabbatar an raba ta da takardunta.

...da fasfon Betta Edu

Wata majiya ta ce haka aka yi da Betta Edu saboda EFCC ta tabbatar da cewa jami’ar gwamnatin ba za ta tsere yayin da ake bincikenta ba.

Vanguard ta tabbatar da an yi awanni ana yi wa tsohuwar kwamishinar ta Kuros Riba tambayoyi game da N585m da aka fitar da umarninta.

Kara karanta wannan

Binciken N37bn: An wuce wurin, Hukumar EFCC ta dauki mataki kan ministar Buhari, ta fadi dalili

Jami’an EFCC sun kuma yi bincike a kan rawar da Akanta Janar ta taka a zargin badakalar.

Wani hali Betta Edu da Sadiya su ke ciki?

Zuwa yanzu babu tabbacin ko Dr. Edu ta bar hedikwatar hukumar yaki da rashin gaskiyar domin ba a iya ji daga bakinta a yammacin jiya ba.

Sannan manema labarai sun yi yunkurin tuntubar lauyar tsohuwar minister watau Sadiya-Farouk, Dipo Okpeseyi SAN, amma ba ayi nasara ba.

Olubunmi Tunji-Ojo da Betta Edu

Kun ji cewa tsohon kamfanin Olubunmi Tunji-Ojo ya samu kwangilar miliyoyi daga wajen Betta Edu a gwamnatin tarayya a shekarar 2023.

Yanzu ana so Bola Tinubu ya dauki mataki, ya bada umarni a binciki Ministan cikin gida kamar yadda EFCC ta ke bincike a kan Dr. Betta Edu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng