Badakalar Kwangila: Mutane Sun Dage Dole a Fatattaki Minista na 2 a Gwamnatin APC

Badakalar Kwangila: Mutane Sun Dage Dole a Fatattaki Minista na 2 a Gwamnatin APC

  • Akwai masu ganin akwai bukatar Shugaba Bola Tinubu ya yi bincike na musamman kan Olubunmi Tunji-Ojo
  • Kamfanin da Ministan ya kafa a shekarun baya ya samu kwangila ta fiye N400m daga wajen gwamnatin tarayya
  • Hon. Olubunmi Tunji-Ojo ya ajiye aiki a kamfanin, amma ana zargin za a iya samun kwangila saboda tasirinsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Wasu mutane sun huro wuta dole sai shugaban kasa ya fatattaki Hon. Olubunmi Tunji-Ojo daga matsayin ministan cikin gida.

Masu wannan kira a kafafen sadarwa na yanar gizo sun ce ya kamata a kori ministan saboda kwangilar da aka ba tsohon kamfaninsa.

Tunji-Ojo
Ministan cikin gida, Bunmi Tunji-Ojo Hoto: @BTOofficial, @edu_betta
Asali: Twitter

Olubunmi Tunji-Ojo zai yi koyi da Nnaji?

Tonye Barcanista ya bada misali da Barth Nnaji wanda ya rasa kujerarsa a lokacin yana Ministan makamashi a mulkin Goodluck Jonathan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Dangote zuwa Otedola: Masu kudin Afrika 20 da adadin Dalolin da suka mallaka a 2024

Gwamnatin Dr. Jonathan ta saida kamfanin wuta ga ‘yan kasuwa, a 2012 aka gano Nnaji ya taba samun alaka da kamfanin Geometric Power.

Duk da ya bar kamfanin lantarkin, a kan haka aka tilastawa ministan yin murabus, kuma NCP ta soke cinikin saboda jin tsoron ayi son kai.

Da yake magana a dandalin X, ‘dan adawan ya bukaci Olubunmi Tunji-Ojo ya yi murabus bayan an gayyace shi zuwa fadar Aso Villa.

...Ana so Tinubu ya binciki Ministansa

Bulama Bukarti wanda masanin shari’a ne a Birtaniya, ya yi irin wannan kira a shafin X, ya ce akwai bukatar dakatar da ministan cikin gidan.

Dalibin shari’ar a jami’ar SOAS yana so shugaban kasa yana so a binciki kwangilolin da aka bada sa’ilin da Betta Edu ta ke kujerar minista.

Ra’ayin lauyan shi ne doka ba amince jami’in gwamnati ya cusa kan shi a inda za a iya samun cin karo tsakanin aikin ofis da ra’ayin kansa ba.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya nuna gwamnan arewa 1, ya bayyana ayyukan Alherin da Yake Zuba Wa Talakawa

Wannan shi ne ra’ayin Yinka Chukwuemeka Ogunnubi, ya ce ko da ministan ya bar kamfanin, ba zai rasa ta-cewa wajen samun kwangila ba.

Tinubu ya soke ma'aikatar jin-kai

Da Legit Hausa ta yi magana da Dr. Mohammed Alhaji, ya ce akwai bukatar a samar da dakunan shan magani a kowace mazaba a Najeriya.

Idan ana so a yi hakan, masanin kiwon lafiyan ya kawo shawarar a soke ma’aikatar jin-kai, a karkatar da kudin zuwa hukumar NPHCDA.

Likitan ya ce wannan zai fi bada damar a binciki idan kudin su ke shiga kuma a iya magance matsalolin kiwon lafiya da ake fama da su.

Olubunmi Tunji-Ojo ya bar kamfaninsa

Olubunmi Tunji-Ojo ne ya kafa kamfanin New Planet Projects Ltd wanda ya samu kwangilar N438m daga ministar jin kai ta kasa.

Ministan harkokin gidan ya ce ya yi murabus daga kamfanin, sai dai ya bar baya da kura da ya ce mai dakinsa ce darektar kamfanin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng