Wacece Sadiya Umar Farouq, matar da ake rade-radin Buhari zai aura

Wacece Sadiya Umar Farouq, matar da ake rade-radin Buhari zai aura

Sadiya Umar Farouq, ita ce ministar sabuwar ma'aikatar jinkai, raya al'umma da kuma kula da aukuwar bala'i, wadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kirkira a zangon gwamnatinsa na biyu.

Babu shakka a 'yan kwanakin nan, ma'abota dandalan sada zumunta na zamani a Najeriya sun ta yada labarin cewa shugaban kasa Buhari zai kara aure kuma ministarsa ta sabuwar ma'aikatar ayyukan agaji da kula da bala'i, Sadiya Umar Farouk za ta kasance amaryarsa.

Wannan rahoto wanda ba'a san tushe ko asalinsa ba, ya yi ta kai komo a fadin kasar, inda har a dandalan sada zumunta irin su Twitter da Facebook aka kirkiri wani maudu'i mai taken #BUSA2019, wato auren shugaban kasa Buhari da Sadiya a shekarar 2019.

Lamarin ya sanya ta kai har an fidda wani katin gayyatar daurin auren shugaba Buhari da Sadiya, inda aka kayyade cewa a ranar 11 ga watan Oktoban da ta gabata ne za'a shafa fatihar auren bayan sallar Juma'a a babban masallaci da ke fadar Villa a birnin Abuja.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, tuni mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Femi Adesina, ya yi watsi da jita-jitar, da cewa shugaban kasar ba aure zai kara ba.

Ga dai wasu muhimman ababe da ya kamata ku sani akan kowace Sadiya Umar Farouk:

An haife ta a ranar 5 ga watan Nuwamban 1974 cikin karamar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

Ta yi karatun sakandire a kwalejin gwamnatin tarayya da ke birnin Gusau na jihar Zamfara, inda kuma ta kammala karaun digiri na farko a fannin nazarin kula da harkokin kasuwanci a jami'ar Ahmadu Bello a shekarar 1998.

Ta kuma samu wasu kwalayen karatun digiri na biyu har kashi biyu a shekarar 2008 da kuma 2011 daga jami'ar ta Ahmadu Bello, inda ta tisa nazarin da tayi akan kula da harkokin kasuwanci da kuma nazari a kan diflomasiyya da harkokin kasashen ketare.

A fannin siyasa kuma, daga shekarar 2011 zuwa 2013, Sadiya ta rike mukamin ma'ajiyar tsohuwar jam'iyyar CPC wadda a cikin ta ne shugaban kasa Buhari ya sha mugunyar kayi a hannun tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a shekarar 2011.

KARANTA KUMA: Ganduje ya zabi kwamishinoni na jihar Kano

Idan ba'a manta ba jam'iyyar CPC na daya daga cikin manyan jam'iyyu hudu da suka gwamutse suka fidda jam'iyyar ACP, wadda ta samu nasarar karbar ragamar jagorancin kasar nan a hannun PDP a shekarar 2015.

Sadiya ta kasance ma'ajiyar jam'iyyar APC ta kasa a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2014, inda kuma daga bisani a ka nada ta a matsayin mamba ta kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar.

Ta kuma kasance tsohuwar shugaba ta cibiyar kula da 'yan gudun hijira da bakin haure haure ta kasa

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng