Ana Daf Da Yanke Hukunci a Kano, Ganduje Ya Nemi Alfarma Daga Yan Adawa a Jihar Arewa

Ana Daf Da Yanke Hukunci a Kano, Ganduje Ya Nemi Alfarma Daga Yan Adawa a Jihar Arewa

  • Shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Dakta Abdullahi Ganduje ya taya Gwamna Alia Hyacinth na jihar Benue murnar nasara a kotu
  • Ganduje ya roki 'yan jam'iyyun adawa da su marawa gwamnan baya don kawo cigaba da kuma ayyukan alkairi a jihar
  • Wannan na zuwa ne yayin da Ganduje ke shirye-shiryen karbar sakamakon hukuncin zaben jiharsa ta haihuwa, Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Benue - Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci 'yan adawa su marawa gwamnatin APC baya a jihar Benue.

Ganduje ya bayyana haka yayin da aka yanke hukuncin zaben jihar inda Gwamna Alia Hyacinth ya samu nasara.

Ganduje ya tura muhimmin sako ga gwamnan APC da jam'iyyun adawa
Ganduje ya taya Gwamna Alia murnar nasara a Kotun Koli. Hoto: Umar Ganduje, Alia Hyacinth.
Asali: Facebook

Yaushe za a yanke hukunci a Kano?

Kara karanta wannan

Kano: Kotun Koli ta tsayar da ranar yanke hukunci kan shari'ar Abba da Gawuna

Wannan na zuwa ne yayin da Ganduje ke shirye-shiryen hukuncin shari'ar zaben gwaman jihar Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana sa ran za a yanke hukuncin a ranar Juma'a 12 ga watan Janairu don raba gardama tsakanin Abba Kabir da Nasiru Gawuna.

Nasiru Gawuna na jam'iyyar APC shi ke kalubalantar zaben Gwamna Abba Kabir na jam'iyyar NNPP.

Shugaban APC ya taya Alia na jihar Benue murnar samun nasara inda ya bukaci hadin kan 'yan adawa a jihar, cewar The Nation.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yada labaransa, Edwin Olofu ya fitar a yau Talata 9 ga watan Janairu.

Ya kirayyi 'yan adawa da su mara masa baya don kawo ci gaba a jihar baki daya ba tare da bambancin siyasa ba, cewar The Guardian.

Mene Ganduje ke cewa?

Kara karanta wannan

Kotun Koli ta tanadi hukunci kan shari'ar karshe ta neman tsige gwamnan PDP, ta ba da bahasi

Yace:

"Wannan nasara ya tabbatar da cewa mutane sun aminta da bangaren shari;a, wannan kuma ci gaban dimukradiyya ce.
"Dukkan magoya bayan mu sun aminta da wannan shugabanci da gwamnan ya ke yi na adalci.
"Lokaci ya yi da dukkan jam'iyyun adawa su zo su hada karfi da karfe don goyon bayan gwamnan a kokarin kawo ci gaba.

Kotu ta yi hukunci kan zaben Benue

A wani labarin, Kotun Koli ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Benue.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Alia Hyacinth na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.