Gwamnan Taraba Ya Saka Sabon Sharadin Daukan Malaman Sakandare Aiki

Gwamnan Taraba Ya Saka Sabon Sharadin Daukan Malaman Sakandare Aiki

  • Gwamna Agbu Kefas ya ce nan gaba kadan za a dakatar da daukar masu kwalin NCE aikin koyarwa a jihar Taraba
  • Kefas ya ce sai masu kwalin 'digiri na biyu' ne kawai za su samu guraben aikin koyarwa a makarantun sakandire
  • Gwamnan ya ce koyarwa a makarantun firamare kuwa, sai mutum na da kwalin digiri na daya kamin ya samu aikin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Taraba - Gwamnan Taraba, Agbu Kefas ya ce zai kawo sabon tsari na kwalin karatu da mutum zai mallaka don neman aikin koyarwa a makarantun firamare da sakandire na jihar.

Kefas ya ce masu kwalin digiri na biyu (masters) ne kawai za a dauka aikin koyarwa a makarantun sakandire a jihar, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

NSCDC ta kama wani matashi saboda bankawa gidaje 4 wuta a Gombe, karin bayani sun fito

Za a sake fasalin koyarwa a makarantun firamare da sakandire a Taraba
Dole malaman sakandire a jihar Taraba su mallaki kwalin digiri na biyu, in ji Gwamna Kefas Hoto: @GovAgbuKefas
Asali: Twitter

Gwamnan ya kuma ce sai kana da kwalin digiri na farko kamin a dauke ka aikin koyarwa a makarantun firamare.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a daina daukar masu kwalin NCE aikin koyarwa a Taraba

Daily Post ta ce Kefas ya bayyana hakan a taron cin abinci da 'yan jarida a Jalingo, a ranar Lahadi, 7 ga watan Janairu.

A cewar sa:

" Nan gaba kadan, masu digiri na farko ne za su koyar a firamare, yayin da masu digiri na biyu za su koyar a sakandire a jihar Taraba."

Gwamnan ya ce an kusa a daina daukar masu kwalin NCE aikin malinta a jihar Taraba.

Kefas ya kuma ce gwamnatin sa za ta saka darasin tarihi a cikin darussan da ya zama wajibi dalibai su koya a makarantun jihar, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mutane 5 wadanda suka fi karfin fada-aji a gwamnatin Buhari da yanzu aka daina jin duriyarsu

Matakin gwamnan abu ne mai kyau amma da kalubale - SYM

Da Legit Hausa ta ji ta bakin Wakilin Daliban Mani, Sanusi Ya'u kan wannan matai da Gwamna Kefa ya dauka, ya ce abu ne mai kyau ma damar za a bi ka'idoji.

A cewar wakilin daliban, mafi akasarin masu kwalin digiri ba su da horo na koyar da dalibai, face wadanda suka karanci harkar koyarwar, don haka ne ma aka fi daukar masu kwalin NCE aiki.

Sanusi Yau ya ce kamata ya yi ace gwamnan ya dauki nauyin malaman da ke kan koyarwa yanzu, su je su karo ilimi, ta yadda za a kara masu karkashin gudanar da aikinsu.

A kyautata albashin malamai - SYM

"Bunkasa harkar ilimi abu ne mai kyau, to amma cewar sai mai kwalin digiri ko masters abu ne mai kalubale, kowa ya san yadda daliban NCE ke goguwa a harkar koyarwa ya zarce na digiri."

Kara karanta wannan

Kwararru sun bayyana dalilai 5 da suka sa yara ke shan wahala a darasin lissafi a makaranta

"Bugu da kari, ko da ace zai dauki masu digiri aiki, ma damar ba a samar masu da kyakkyawan yanayi ba, da albashi mai tsoka, to abin da ya guda din shi ne zai ci gaba da faruwa.

A cewar wakilin daliban.

NNPP ta daukaka kara zuwa Kotun Koli kan shari'ar gwamnan Taraba

A wani labarin, jam'iyyar NNPP da dan takararta Farfesa Sani Yahaya sun ce ba za su amince da hukuncin Kotun Daukaka Kara kan shari'ar zaben gwamnan jihar Taraba ba.

Sani Yahaya da NNPP sun tattara kan lauyoyin su, sun garzaya Kotun Koli inda su ka ce za a kwato masu hakkinsu domin su ne suka lashe zaben gwamnan jihar ba Kefas ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.