Sabuwar doka: Ma su digiri mai daraja ta farko da ta biyu kadai za'a bawa aikin koyarwa; FG
- Aikin koyarwa zai koma sai masu shaidar kammala digiri mai daraja ta daya ko ma fi girman daraja ta biyu
- Gwamnatin tarayya ta ce tuni shirye-shiryen kaddamar da dokar sun yi nisa
- A cewar babbar sakatare a ma'aikatar ilimi, sabuwar dokar za ta shafi dukkan makarantun sakandire hatta masu zaman kansu
Gwamnatin Najeriya na shirin kafa dokar daukan masu babban matakin digiri na biyu a matsayin mafi ƙarancin cancanta don zama malamin makaranta.
Gwamnatin tarayya a ranar Asabar a Abuja ta ce shirye-shirye na kan hanya don ganin an yi wani tsari ga malaman makaranta nan gaba, wanda matakin digiri mai daraja ta ɗaya ko babban matakin digiri mai daraja ta biyu ya zama mafi ƙarancin cancanta don zama malami.
Sakataren din-din-din a ma'aikatar ilimi, Sonny Echono, ne ya faɗi hakan lokacin da yake kula da yadda ake gudanar da jarrabawar ƙwarewar aiki (PQE) wadda hukumar yiwa malamai rijista ta Najeriya(TRCN) ta tsara.
Acewarsa, tsarin zai taimaka wajen jijjige balagurbin malamai daga makarantun ƙasar nan.
Ya ƙara da cewar za'a kafa kwamitin aiwatar da wannan dokar a ƙasa bakiɗaya nan bada jimawa ba.
Malam Echono ya ce, "mu na tsara bawa masu digiri mai mataki na ɗaya da masu babban matakin digiri mai mataki na biyu hanyar shigowa a matsayin mafi ƙaranchin cancantar da zamu ɗauka, kuma tuni muka maida hankali don ganin mun aiwatar da dokar.
"Koda kana makarantu masu zaman kansu, na gwamnati, na al-umma ko na addinai, za mu tabbatar da ɗabbaƙa wannan dokar akan kowa.
"Abu na farko da zai faru, shine hukumomin TRCN da NTI su tattaro jadawalin malamai da suka cancanta."
"Ina nufin, wanda aka basu shaida, kuma suka tsallake wannan jarrabawar amna basu da aikin yi." a cewarsa.
Ya ƙara da cewar; "mu na tsara inganta albashin malamai masu ɗaukar kimiyya, da kuma ƙarin alawus ga masu koyar da masu buƙata ta musamman.
"Yanzu haka muna aiki akan albashin malamai na musamman da ke koyar da masu buƙata ta musamman.
"Mu na shirin kawo ƙarshen adadin ƙidayar mu tare da hukumar albashi da ladan aiki,a maganar da muke yanzu haka an samar da wasu.
"Mu na aiki da masu ruwa da tsaki don gabatar da jawabi tare da NUT. Mu na kuma ƙoƙarin jin ra'ayin masu ɗaukar ma'aikata kamar gwamnatocin jihohi da kuma masu makarantu masu zaman kansu."
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng