Shirin S-Power na gwamnatin jihar Katsina zai samar da aiki ga masu kwalin NCE 5,000 - Gwamna Masari
- Gwamnatin jihar Katsina ta ce za ta dauki masu shaidar karatun NCE 5,000 aiki
- Gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, ya sanar da haka
- Ya ce ya kwaikwayi shirin gwamnatin tarayya na N-POWER ne
Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ta ce gwamnatinsa za ta dauki masu shaidar kammala karatun NCE har 5,000 aikin koyarwa a makarantun firamare.
Gwamna Masari ya sanar da haka ne yau a karamar hukumar Rimi yayin wani taron karbar magoya bayan jam'iyyar PDP da suka canja sheka zuwa jam'iyyar APC.
Gwamnan ya bayyana cewar, ya kwaikwayi shirin N-POWER na gwamnatin tarayya da ya samar da aikin yi ga matasa 500,000.
Ya ce shirin na daga cikin kokarin gwamnatinsa na samar da aikin yi ga matasa da kuma bunkasa ilimi, kamar yadda ya yi alkawari yayin yakin neman zabe.
DUBA WANNAN: Dokar hana Fulani makiyaya kiwo a jihar Benuwe: Gwamna Ortom ya bayar da umarnin kama Fulani makiyaya
Yayin taron karbar magoya bayan jam'iyyar PDP da suka canja sheka, gwamna Masari ya nuna gamsuwa da dandazon magoya baya da suka halarci wurin taron.
Kazalika shugaban jam'iyyar APC a jihar Katsina, Shitu S. Shitu, ya bayyana cewar salon mulkin gwamna Masari ne ya jawo hankalin jama'a har suke tururuwar shiga jam'iyyar APC a jihar.
Daya daga jama'ar da suka canja sheka ya zuwa jam'iyyar APC, Bilyaminu Rimi, ya bawa gwamnan tabbacin bayar da gudunmawa a kowanne fanni domin ciyar da jihar gaba.
Rahotanni sun bayyana cewar gwamna Masari na shiye-shiryen canja wasu kwamishinoninsa da sababbin 'yan siyasar da suka canja sheka, domin kara bunkasa damar cin zabe a shekarar 2019.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng