Jerin Manyan Mata Yan Siyasa 7 da Aka Zarga da Cin Hanci a Najeriya
A 'yan kwanakin nan, badakalar makudan kudade da aka samu wasu mata masu rike da mukamai a Najeriya ya saka shakku kan shugabancin mata a kasar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Hukumar EFCC yanzu haka ta na tuhumar tsohuwar ministar jin-kai, Sadiya Umar da dakatacciyar Shugabar hukumar NSIPA, Halima Shehu kan badakalar kudade.
Har ila yau, a jiya Litinin Shugaba Tinubu ya dakatar da Ministar jin kai, Dakta Betta Edu tare da fara bincike a kanta.
Legit Hausa ta jero muku jerin mata da ake zarginsu da wawushe makudan kudade a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Sadiya Umar Farouk
Tsohuwar Ministar jin kai da walwala ta shiga hannun hukumar EFCC kan zargin karkatar da biliyan 37 lokacin da ta ke rike da mukamin.
Ana zargin ta karkatar da kudaden ne ta hannun dan kwangila inda a yanzu haka ta na ganawa da EFCC a Abuja.
2. Dakta Betta Edu
A jiya Litinin ce Shugaba Tinubu ya dakatar da ita saboda zargin karkatar da miliyan 585 zuwa wani asusun banki na daban.
Ministar a jiya ta yi kokarin ganin Tinubu amma jami'an tsaron Aso Rock sun hana ta ganin shugaban tare da kwace katin shaidar shiga fadar.
Edu ta umarci Akanta Janar ta tura kudaden zuwa asusun bankin inda ita kuma ta ce ba ta bi umarnin Ministar ba.
3. Halima Shehu
Shugaba Tinubu ya dakatar da ita a matsayin shugabar hukumar NSIPA kan zargin wawure biliyan 44, cewar BusinessDay.
Ana zargin Halima ta tura kudaden ne zuwa wasu asusun bankuna inda ta ce ta yi hakan ne saboda matsin lamba daga Minista Betta Edu.
4. Muheeba Dankaka
Ana zargin Muheeba da karbar miliyoyin kudade wurin neman aiki a Najeriya a Hukumar Raba Dai-dai da take jagoranta.
Muheeba dai ta musanta zargin da ake yi a kanta inda ta yi rantsuwa a gaban kwamitin Majalisar Dokoki yayin bincike.
5. Hadiza Bala Usman
Ana zargin Bala Usman wacce itace tsohuwar shugabar hukumar jiragen ruwa da karkatar da biliyoyin kudade, cewar Punch.
Daga bisani an dakatar da ita don gudanar da bincike yayin da ita kuma ta musanta zargin da ake yi mata.
6. Diezani Alison-Madueke
An dade ana shari'a kan badakalar makudan kudade kan tsohuwar Ministar man fetur fiye da shekaru 10.
Diezani ta tsere kasar Burtaniya inda a can din ma ta ke fuskantar shari'a kan wasu korafe-korafe.
7. Stella Oduah
Tsohuwar Ministar jiragen sama a mulkin Jonathan ta fuskanci zargin karkatar da biliyoyin kudade, cewar Premium Times.
Sanata Oduah daga bisani ta samu nasarar kasancewa Sanata a lokacin mulkin Muhammadu Buhari bayan kai-komo a shari'ar.
An hana Edu ganawa da Tinubu
A wani labarin, dakatacciyar Ministar jin kai a Najeriya, Betta Edu ta samu matsala a fadar shugaban kasa.
Jami'an tsaron fadar sun hana ta shiga fadar ce bayan an dakatar da ita kan badakalar kudade.
Asali: Legit.ng