Kungiyar CAN Ta Fusata Kan Hare-hare a Arewa, Ta Jagoranci Zanga-zanga Don Nuna Bacin Ranta
- Shugaban kungiyar CAN a jihar Plateau, Rabaran Polycarp Lubo ya jagoranci zanga-zanga kan hare-haren 'yan bindiga a jihar
- Kungiyar reshen jihar ta dauki matakin ne don nuna rashin jin dadi kan hare-haren da ya ki ci ya ki cinyewa a fadin jihar
- Hakan ya biyo bayan hallaka mutane fiye da 200 da 'yan bindiga suka yi a karshen watan Disambar 2023 a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Plateau - Kungiyar Kiristoci a Najeriya (CAN) a yanzu haka ta na jagorantar zanga-zanga a Jos da ke jihar Plateau.
Kungiyar reshen jihar ta dauki matakin ne don nuna rashin jin dadi kan hare-haren da ya ki ci ya ki cinyewa a fadin jihar, cewar Vanguard.
Mene dalilin daukar matakin Kungiyar CAN?
Shugaban kungiyar a jihar, Rabaran Polycarp Lubo shi ke jagorantar zanga-zangar tare da shugaban ECWA, Rabaran Dakta Stephen Baba Panya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran sun hada da shugaban majami'ar COCIN, Rabaran Dakta Amos Mohzo da shugaban cocin Methodist, Rabaran Nkechi Nwosu da sauran shugabannin Kiristoci a jihar.
Wannan na zuwa ne bayan hare-haren bindiga da ya addabi jihar musamman a yankunan karkara, Punch ta tattaro.
'Yan sanda sun cafke wasu mutane a Plateau
A ranar jajiberin Kirsimeti, mahara sun hallaka mutane fiye da 200 a wani kauye da ke jihar wanda ya ta da hankula matuka a kasar.
Masu zanga-zangar sun fara tattakin ne daga shatatalen PRTVC inda suka nufi gidan gwamnatin jihar don nuna rashin jin dadinsu kan hare-haren.
Rundunar 'yan sanda a jihar ta sanar da cafke wasu mutane takwas da ake zargi da hannu a kai harin na watan Disamba, cewar Daily Post.
Kakakin rundunar a jihar, Alfred Alabo ya ce an samu zaman lafiya a yankin da aka kai harin bayan cafke mutanen.
'Yan sanda sun cafke kwararriyar mai satar waya
A wani labarin, rundunar 'yan sanda a jihar Borno ta tabbatar da cafke wata mata da ta kware a satar waya a birnin Maiduguri.
Matar mai suna Fatima Abacha da aka fi sani da 'Bintu' ta shiga hannu ne da wasu mutane 84 a jihar.
Matar ta bayyana yadda ta ke satar wayar tata cikin hikima ba tare da an ankara da ita ba.
Asali: Legit.ng