“Ba Zama”: Gwamnan Jihar Arewa Ya Yi Ganawar Sirri da Shugaba Tinubu a Abuja, an Gano Dalili

“Ba Zama”: Gwamnan Jihar Arewa Ya Yi Ganawar Sirri da Shugaba Tinubu a Abuja, an Gano Dalili

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya sha alwashin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin al'ummar Najeriya
  • Tinubu ya dauki alkawarin ne lokacin da ya gana da gwamna Buni, wanda ya ziyarce shi kan matsalar tsaro a Yobe
  • Kafin ganawarsa da shugaban kasar, Buni ya fara haduwa da ministan harkokin 'yan sanda, Sanata Ibrahim Gaidam a Abuja

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa don tattauna matsalar tsaro da ta addabi jiharsa.

Daraktan watsa labarai na gwamnan, Alhaji Mamman Mohammed ya fitar da sanarwar hakan, inda ya ce Buni ya kuma hadu da ministan harkokin 'yan sanda, Sanata Ibrahim Gaidam.

Kara karanta wannan

Akwai kitimutmura a 2027: Tawagar G5 ta PDP a ta marawa shugaba Tinubu baya a zaben 2027, Inji Ortom

Gwamnan Yobe ya gana da Shugaban kasa
Matsalar tsaro a Yobe: Gwamna Buni ya yi wa Tinubu sammako, ya nemi taimakon fadar shugaban kasa. Hoto: @KaitafiS
Asali: Twitter

Gwamna Buni ya gana da Sanata Gaidam

Gwamnan da ministan sun tabbatar da cewa an samu tsaro a 'yan kwanakin nan, amma sun duba yiwuwar kawo sabbin tsare-tsare na inganta tsaron a fadin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Leadership ta ruwaito cewa Buni da Gaidam sun garzaya fadar shugaban kasar, inda suka tattauna da Shugaba Tinubu, kan hanyoyin kawo karshen matsalar tsaro a Yobe.

Gwamnan ya ce:

"Duk da an samu tsaro a jihar, sai dai akwai garuruwan da ke iyakokin jihar da ke fuskantar hare-hare, mun dauki matakan dakile 'yan ta'adda daga shigowa cikin jihar."

Abin da Shugaba Tinubu ya fadi wa Gwamna Buni

Buni ya ci gaba da cewa:

"Ba shakka an samu tsaro a Yobe, musamman cikin birane, sai dai har yanzu wasu kauyuka na fuskantar barazanar 'yan ta'adda."

A cewar sanarwar, Shugaba Tinubu ya tabbatar wa gwamnan cewa gwamnatinsa za ta yi duk mai yiyuwa don inganta tsaro a Najeriya, a cewar rahoton Independent.

Kara karanta wannan

'Ba zan lamunci rashin nasara daga gareku ba', Tinubu ya kyankyasa gargadi ga manyan sojojin kasa

Yan sanda sun kama magidanci kan zargin kashe matarsa a Yobe

A wani labarin, 'yan sanda sun kama wani magidanci mai suna Abubakar Musa, bisa zargin ya kashe matarsa Ammi Mamman a garin Damaturu, babban birnin jihar Yobe.

Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargin ya kashe matarsa ne ta hanyar daba mata wuka a wuya, lokacin da suke kwance a kan gado a yammacin ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.