Gwamnan Yobe Ya Gana da Shugaban Hafsoshin Tsaro Kan Batun Boko Haram a Geidam

Gwamnan Yobe Ya Gana da Shugaban Hafsoshin Tsaro Kan Batun Boko Haram a Geidam

- Gwamna Buni ya gana masu ruwa da tsaki don tabbatar da zaman lafiya a yankin Geidam

- Gwamnan ya tattauna da shugaban hafsoshin tsaro kan mafita mai dorewa ga lamarin tsaro

- Gwamnan ya bayyana cewa, dole ne a matsayinsa na jagora ya nemo hanyoyin magance tsaro

KU KARANTA: 'Yan Bindiga Sun yi Awon Gaba da Mutane 35, Sun Sace Shanu da Dama a Jihar Neja

Gwamnan jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, a ranar Lahadi ya gana da shugaban hafsoshin tsaro Janar Leo Irabo don tattauna batun harin Boko Haram a Geidam.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Darakta Janar na harkokin yada labarai ga Gwamnan, Mamman Mohammed ya sanya wa hannu a ranar Lahadi, Vanguard News ta ruwaito.

Mohammed ya ce, tun daga ranar Juma'a ne Buni ya kasance yana tattaunawa da jami'an tsaro don samar da mafita mai dorewa game da kai hare-hare a kan Geidam da al'ummomin kan iyaka.

KU KARANTA: Yariman Saudiyya ya Magantu da Mahamat Idriss Deby kan Rasuwar Mahaifinsa

Gwamnan Yobe Ya Gana da Shugaban Hafsoshin Tsaro Kan Batun Boko Haram a Geidam
Gwamnan Yobe Ya Gana da Shugaban Hafsoshin Tsaro Kan Batun Boko Haram a Geidam Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Gwamna Buni ya ce akwai bukatar gaggauta samar da mafita ta din-din-din game da kutsen da masu tayar da kayar baya ke yi a cikin jihar.

“Matsalar da muke da ita ita ce motsawar masu tayar da kayar baya daga gabar Tafkin Chadi zuwa cikin jihar.

"Muna bukatar duba wannan lamarin gaba daya don magance matsalar din-din-din," in ji shi.

Ya koka da cewa mutanen Geidam sun sha fuskantar hare-hare da dama da kuma wahalhalun da ba za a iya fada ba wanda ya zama dole a dubesu da idon tausayawa.

Gwamna Buni ya ce "A matsayina na jagora, dole ne in binciko duk hanyoyin da suka hada da ganawa da Shugaban Hafsoshin Tsaro da shugabannin rundunonin tsaro domin tabbatar da tsaro da lafiyar mutanen Geidam da jihar baki daya."

KU KARANTA: Allah-wadai: Biyo bayan kashe mambobinta, IPOB ta yi babban gargadi ga gwamnati

A wani labarin, Ana ci gaba da luguden wuta tsakanin sojojin Najeriya da masu tayar da kayar baya na kungiyar ISWAP a Geidam, jihar Yobe, Arewa maso gabashin Najeriya.

'Yan ta'addan sun dawo garin Geidam ne 'yan sa'o'i bayan da suka janye bayan da aka shafe sama da awanni 24 suna yi wa garin kawanya, farawa daga ranar Juma'a, 23 ga Afrilu.

An samu labarin a safiyar Lahadi cewa sojojin Najeriya da masu tayar da kayar baya a halin yanzu suna artabu sosai sakamakon wani sabon hari.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel