Don Burge Bankin Duniya: An Tona Asirin Dalilin Tinubu Kan Kara Farashin Mai Da Wutar Lantarki
- An gano babban dalilin da ya saka Gwamnatin Tarayya ta ke kokarin kara farashin man fetur da kuma wutar lantarki
- Kungiyar CHRICED ta bayyana cewa Tinubu ya na neman dadada wa Bankin Duniya ne musamman irin kalamansu kan farashin mai a watan Disamba
- Babban daraktan hukumar, Ibrahim Zikirullahi shi ya bayyana haka a jiya Juma'a 5 ga watan Janairu
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam da Wayar da Kan Jama'a (CHRICED) ta yi gargadi kan kara kudin wutar lantarki da man fetur.
Kungiyar ta bayyana babbar matsalar da za a samu kan matakin Tinubu wanda zai shafi tattalin arzikin Najeriya da gurgunta ta.
Mene dalilin karin farashin mai da wutar lantarki?
Babban daraktan hukumar, Ibrahim Zikirullahi shi ya bayyana haka a jiya Juma'a 5 ga watan Janairu, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ibrahim ya ce wannan kare-karen farashin mai da wutar lantarki an yi ne don dadada wa Bankin Duniya.
Ya ce abin takaici ne yadda ake kare-karen kudaden wanda ke shafar talaka kai tsaye tare da gurgunta tattalin arziki.
Zikirullahi ya ce duk da kamfanonin NNPCL da NERC sun karyata jita-jitar amma bisa ga dukkan alamu akwai kamshin gaskiya a jita-jitar, cewar Vanguard.
Gargadin da kungiyar ta yi
Ya ce:
"Kamar yadda ake fada idan ba rami mai ya kawo maganar rami, su na son gwada 'yan Najeriya ne don ganin yadda za su yi martani.
"Ganin yadda ake gaba a dawo baya kan kare-karen kudaden ya tabbata akwai kamshin gaskiya a ciki.
"Idan ba a mantaba a watan Disamba, Bankin Duniya ta yi maganar cewa ya kamata litar mai ta kai naira 750."
Ministar Tinubu ya fada wata badakala
A wani labarin, ana zargin Ministar jin kai da walwala, Dakta Betta Edu da umartar tura mata wasu kudade asusun banki na musamman.
An leko wata takarda da Ministar ta umarci Akanta Janar ta tura kudaden har naira miliyan 585 zuwa wani asusun bankin UBA.
Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da tuhumar tsohuwar Ministar jin kai da walwala, Sadiya Umar Farouk kan badakalar biliyan 37.
Asali: Legit.ng