Bayanai Sun Fito Yayin da Gwamnoni 2 Su Ka Zauna da Tinubu a Fadar Aso Villa
- Gwamnonin jihohin Neja da Gombe sun ziyarci fadar Aso Rock Villa a karshen makon nan a Abuja
- Umar Mohammed Bago da Inuwa Yahaya sun samu damar ganin Mai girma Bola Ahmed Tinubu
- Makasudin zuwan gwamnonin fadar shugaban kasa shi ne ganin yadda za a bunkasa harkar noma
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - A ranar Alhamis, gwamnan Neja, Umar Mohammed Bago da takwaransa na Gombe, Inuwa Yahaya, su ka je fadar Aso Rock Villa.
Premium Times ta ce gwamnonin jihohin biyu sun gana da Mai girma Bola Ahmed Tinubu a mabanbantan lokuta a fadar shugaban Najeriya.
Bola Ahmed Tinubu da shirin noma
Gwamnonin sun yi magana da shugaba Bola Ahmed Tinubu ne a kan yadda za su hada-kai da gwamnatin tarayya domin a samu abinci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A jawabinsa na shiga sabuwar shekara, Bola Tinubu ya nuna muhimmancin yin noma.
Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Bola Tinubu ta sa ran amfani da eka 500, 000 wajen yin noma a shekarar nan da aka shiga.
A dalilin haka ne gwamna Umar Bago ya ce an tanadi fili a jihar Neja domin noman rani.
Kokarin gwamnan jihar Neja
Gwamnatin jihar Neja ta shiga yarjejeniya da kamfanin Tata Group da hukumar NASENI domin a bunkasa harkar noma a shekarar nan.
Mai girma Umar Bago ya ce idan su ka hada-kai da gwamnatin tarayya, mutanensa za su samar da buhunan abinci kamar yadda ake buri.
...Gwamna Inuwa Yahaya
Rahoton NAN ya ce Inuwa Yahaya ya shaidawa 'yan jarida ya zo ganin shugaban kasa ne domin sanar da shi yadda ake ciki a Gombe.
Gwamna Yahaya yake cewa akwai bukatar jiharsa ta hada-kai da gwamnatin tarayya musamman ganin an amince da kasafin kudi.
Gwamnan ya gabatarwa shugaban kasa nasarorin da ya samu a mulki, ya fadi rawan da za su taka domin a noma isasshen kayan abinci.
Tsohon gwamna ya fasa kwai
Kun samu labari an yi wa baitul-mali wayam har ta kai tsohuwar gwamnati tana cin bashi domin a iya biyan albashi, babu komai a asusu.
Cif Segun Osoba ya ce wajibin Bola Ahmed Tinubu ya nemo bashin kudi domin kuwa babu kudin gudanar da ayyuka da ya shiga Aso Villa.
Asali: Legit.ng