Shugaba Tinubu Ya Tsige Shugaban NASENI, Ya Nada Wani Mai Shekara 32

Shugaba Tinubu Ya Tsige Shugaban NASENI, Ya Nada Wani Mai Shekara 32

  • Shugabancin Dr. Bashir Gwandu a hukumar NASENI ya zo karshe daga Satumban nan na 2023
  • Bola Ahmed Tinubu ya dauko Khalil Suleiman Halilu a matsayin sabon shugaban hukumar kasar
  • Ajuri Ngelale ya fitar da sanarwar nada ‘dan shekara 32 da haihuwa da yawun shugaban kasa

Bola Ahmed Tinubu ya sallami Dr. Bashir Gwandu daga kujerar da ya ke kai ta babban shugaban hukumar nan ta NASENI.

Mai taimakawa shugaban Najeriya wajen yada labarai da hulda da jama’a, Ajuri Ngelale, ya sanar da haka a yammacin Juma’a.

Ajuri Ngelale ya ce wanda zai maye gurbin Gwandu a NASENI shi ne Khalil Suleiman Halilu.

NASENI
Shugaban NASENI, Khalil Suleiman Halilu Hoto: @DOlusegun, @NGRPresident
Asali: UGC

Gwamnatin tarayya ta kafa wannan hukumar ne domin kula da kimiyya a bangaren samar da abubuwan more rayuwa a Najeriya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Sake Ware Biliyoyin Kudade Don Sake Gina Arewa, Ya Bayyana Dalili

Khalil Suleiman Halilu

Kamar yadda jawabi ya fito daga fadar shugaban Najeriya dazu, Khalil Suleiman Halilu zai yi shekara biyar a kan mukamin.

Kamar yadda dokokin NASENI na 2014 su ka yi tanadi, sabon shugaban zai iya zarcewa kan kujerar bayan wa’adin farko ya kare.

Da wannan nadin mukami da aka fitar a ranar 1 ga Satumban 2023, wa’adin Khalil Halilu mai shekara 32 zai kare ne a 2028.

Cif Ngelale ya ce ana sa ran sabon shugaban hukumar ya yi amfani da kwarewarsa wajen kawo cigaba a hukumar tarayyar.

Matashi ya samu shiga

Makonni bayan nada ministoci, da wannan umarni na shugaban kasa, nadin mukamin ya fara aiki ba tare da bata lokaci ba.

Watakila Mista Khalil shi ne mai mafi karancin shekaru a wadanda Bola Ahmed Tinubu ya ba mukami bayan hawansa kan mulki.

Tasirin cire tallafin fetur

Dazu nan rahoto cewa kamfanin mai na NNPC ya bayyana asarar da ya tafka bayan cire tallafin man fetur da aka yi a Mayun 2023.

NNPC ya ce an samu raguwar amfani da man fetur a Najeriya da 30%. Hakan ya nuna mutane da-dama sun fara hakura da shan mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng