‘Yan Majalisa na Yunkurin Kirkiro Sababbin Jami’oi 47 Lokaci Daya a Jihohi

‘Yan Majalisa na Yunkurin Kirkiro Sababbin Jami’oi 47 Lokaci Daya a Jihohi

  • ‘Yan majalisar wakilai da dattawa sun gabatar da kudirin da za su iya jawo a kafa karin makarantu
  • Idan kudirin sun zama dokoki, za a ga karuwar jami’o’in tarayya zuwa kusan 100 kenan a Najeriya
  • Bayan jami’o’i, akwai yunkurin gina sababbin makarantun da ake kira FCE da Poly a jihohin kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Adadin jami’o’in gwamnatin tarayya za su iya tashi nan da ‘yan watanni idan ‘yan majalisa su ka samu yadda suke so.

Punch ta ce yanzu haka ana tafka muhawara a majalisar tarayya domin a kafa wasu sababbin jami’o’i 47 a fadin Najeriya.

'Yan majalisa
Sanatoci da ‘Yan Majalisa na so a kara jami'o'i Hoto: @HouseNgr, @NgrSenate
Asali: Twitter

Adadin jami'o'in tarayya za su kai 99?

Idan ‘yan majalisar suka yi nasara, adadin jami’o’in gwamnatin tarayya za su kai 99 bayan jami'o'in 'yan kasuwa fiye da 100.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamna Abba ya samu gagarumin goyon baya yayin da Kotun Koli ke dab da yanke hukunci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yanzu haka akwai jami’o’in tarayya 25 da ke jihohi 36 da birnin Abuja. A wasu jihohin akwai jami’o’in tarayya fiye da guda a yau.

Karin makarantu da asibitocin gwamnati

Baya ga kokarin kara yawan makarantu, ana muhawara a majalisar kasar domin kafa manyan asibitocin tarayya 56 a jihohi.

Abin bai tsaya nan ba, ‘yan majalisar sun dage wajen ganin an kirkiro makarantun koyon karantarwa na FCE akalla 32 a kasar.

Baya ga haka ana so gwamnatin tarayya ta gina wasu makarantun koyon aikin gona 11 da manyan makarantun koyon aiki biyar.

Yanzu maganar da ake yi, akwai asibitocin tarayya na FMC fiye da 22 da FCE har 27 da kuma makarantun ‘Poly’ 40 a Najeriya.

Kwanaki har ta kai ana zargin gwamnati da son kai wajen gina asibitocin tarayya a kasar.

Rahoton ya ce ‘yan majalisar su na kawo kudiri domin kafa makarantu da cibiyoyin koyon sana’o’i na musamman a mazabunsu.

Kara karanta wannan

NUC ta fitar da cikakken jerin sunayen jami'o'in da aka haramta a Najeriya

‘Yan majalisar kasar sun maida shi al’ada, su rika kawo kudirin gina sababbin makarantu da asibitoci a yankunan da su ka fito.

Daga cikin makarantun nan akwai na ilmin kimiyya da fasaha, aikin gona, koyon tukin jirgin sama, kiwon lafiya da dai sauransu.

EFCC v Sadiya Umar-Farouq

Jami'an EFCC sun ce ba su karbi uzurin rashin lafiyar tsohuwar Ministar Muhammadu Buhari watau Sadiya Umar-Farouq ba.

Dole Hajiya Sadiya Umar-Farouq ta amsa tambayoyin da za ayi mata nan da safiyar ranar Laraba mai zuwa ko kuwa a dauki mataki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel