Buhari ya nada dan Arewa mukamin shugaban hukumar NIMASA

Buhari ya nada dan Arewa mukamin shugaban hukumar NIMASA

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sabon shugaban hukumar kula da masana’antar ruwa ta Najeriya, NIMASA, sakamakon karewar wa’adin tsohon shugaban hukumar, Dakta Dakuku Peterside.

Shugaba Buhari ya maye gurbin Dakuku ne da wani babban jami’in hukumar da ya fito daga yankin Arewacin Najeriya, Dakta Bashir Jamoh, wanda kafin nan shi ne daraktan kudi da al’amuran mulki na hukumar NIMASA.

KU KARANTA: Annobar Coronavirus: Sultan ya bukaci Musulmai su fara addu’o’in neman agaji daga Allah

Buhari ya nada dan Arewa mukamin shugaban hukumar NIMASA
Bashir
Asali: Facebook

As shekarar 2016 ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Dakuku mukamin shugabancin NIMASA, kuma a ranar 10 ga watan Maris na shekarar 2020 ne wa’adin mulkinsa ke karewa.

Bashir Jamoh dan asalin jahar Kaduna ne, kuma shugaban cibiyar kwararrun masu kula da sha’anin sufuri a Najeriya, CIOTA. Kuma ya samu kammala digirin digirgir daga jami’ar Fatakwali.

Bashir ya yi karatun diploma a jami’ar Ahmadu Bello, daga nan ya samu shaidar kammala babbar diploma a jami’ar Bayero ta Kano, daga nan kuma ya yi karatun digiri na biyu a jami’ar kasar Korea.

Bashir Jamo ya fara aiki da gwamnatin jahar Kaduna, inda daga bisani ya tsallake ya koma hukumar NIMASA a 1994, a yanzu ya kwashe tsawon shekaru 32 yana aiki a masana’antar sufurin ruwa, ya wallafa littafi daya danganci ciyar da masana’antar gaba.

A wani labarin kuma, Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana damuwarsa game da bullar annobar cutar Coronavirus a Najeriya da ma duniya gaba daya, do haka ya yi kira ga Musulmai su gudanar da addu’o’I na musamman.

Sultan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da sakataren kungiyar Jama’atil Nasril Islam, JNI, Dakta Khalid Abubakar Aliyu ya fitar a ranar Laraba, 4 ga watan Maris a garin Kaduna.

Sultan ya yi kira ga Musulmai su dage da tsafta tare da bin duk wasu hanyoyin tsaftace kawunansu don kauce ma yada cutar Coronavirus, sa’annan ya yi kira ga Malamai da limamai su cigaba da wayar da kawunan jama’a akan cutar a dukkanin salloli biyar na kowanne rana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel