Cikakken Jerin Jami'o'in Kasashen Waje da Gwamnatin Tinubu Ta Haramta a Najeriya
- Ingancin ilimi da yawan manyan makarantu da malamai ya ƙaru a hankali a cikin ƙarni na 21 da muke ciki
- Duk da haka, akwai alamun rashin gaskiya a cikin tsarin ilimi na yanzu a yankin nahiyar Afirika inda ake samun takardun bogi
- Ɗaya daga cikin rashin halascin shi ne batun cibiyoyi masu bayar digiri, waɗanda basu cika ƙa'ida ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - A ranar Talata, 2 ga watan Janairu, 2024, gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da tantancewa da amincewa da takardun shaidar digiri daga jamhuriyar Benin da Togo.
Dakatarwar ta biyo bayan rahoton binciken da wata jarida ta intanet ta yi, wanda ya bankaɗo wata jami'ar Cotonou.
Jami’ar ta bayar da takardar shaidar digiri ga wani ɗan jarida a ɓoye cikin makonni shida.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
FG ta yaƙi takardun bogi na jami'o'in ƙasashen waje
A cewar gwamnatin Bola Tinubu, dakatarwar za ta cigaba har zuwa samun sakamakon binciken da aka fara gudanarwa.
Binciken dai ya ƙunshi ma’aikatun harkokin waje da ilimi na Najeriya da na ƙasashen biyu da kuma hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), da kuma hukumar yi wa ƙasa hidima (NYSC).
Biyo bayan hakan, Legit.ng ta yi ƙarin haske kan jerin sunayen jami'o'in ƙasashen waje da hukumar kula da jami'o'i ta ƙasa (NUC) ta haramta.
Duba su a nan ƙasa:
1. Kwalejin Jami'ar Volta, Ho, Yankin Volta, Ghana. Da duk wasu cibiyoyinta a Najeriya.
2. Jami'ar Columbus, UK da duk inda take aiki a ko'ina a Najeriya.
3. Jami'ar Pebbles, UK da duk inda take aiki a ko'ina a Najeriya.
4. Jami'ar Pilgrims da duk inda take aiki a ko'ina a Najeriya.
5. Jami'ar EC-Council University, Amurka, da cibiyar karatunta dake Ikeja, Legas.
6. Jami'ar Houdegbe ta Arewacin Amurka da ke Najeriya.
7. Jami'ar Ilimi, Winneba Ghana, da duk inda take aiki a ko'ina cikin Najeriya.
8. Jami'ar African University Cooperative Development, Cotonou, Jamhuriyar Benin, da duk inda take aiki a ko'ina cikin Najeriya.
9. Jami'ar Evangel ta Amurka da Kwalejin Gudanarwa ta Chudick, Legas.
10. University of Applied Sciences and Management, Port Novo, Jamhuriyar Benin da dukkanin rassanta dake a Najeriya.
11. Jami'ar ƙasa da ƙasa, Missouri, Amurka, Kano da cibiyar nazarinta ta Legas, ko kuma wasu cibiyoyi nata a Najeriya.
12. Tiu International University, UK da duk inda take aiki a ko'ina a Najeriya.
13. London External Studies UK da duk inda take aiki a ko'ina a Najeriya.
14. Jami'ar West African Christian University da duk inda take aiki a ko'ina a Najeriya.
15. Jami'ar Concept College/Universities (Landan) Ilorin da duk rassanta dake Najeriya
16. Jami'ar Irish University Business School Landan, da duk inda take aiki a ko'ina cikin Najeriya.
17. Jami'ar Cape Coast, Ghana, da duk inda take aiki a ko'ina cikin Najeriya.
18. Jami'ar Pacific Western University, Denver, Colorado, da cibiyar nazarinta dake Owerri.
Jerin Jami'o'in da Suka Fi Kyau a Afirika
A wani labarin kuma, kun ji cewa an fitar da jerin jami'o'in da suka fi kyau a shekarar 2023 a nahiyar Afirika.
Jami'o'in Najeriya guda biyu waɗana suka haɗa da jami'ar Covenant da jami'ar Ibadan ne suka samu shiga cikin jerin.
Asali: Legit.ng