Kano: Hukumar Hisbah Ta Kama Babbar Mota Dauke da Kwalabe 24,000 Na Barasa

Kano: Hukumar Hisbah Ta Kama Babbar Mota Dauke da Kwalabe 24,000 Na Barasa

  • Akalla kwalaben giya dubu 24 ne hukumar Hisba ta jihar Kano ta kwace yayin da ta cafke wata babbar mota a hanyar Kano zuwa Zariya
  • A cewar hukumar, jami'an Hisba ba za su yi kasa a guiwa ba wajen tabbatar da tsarin shari'a a jihar Kano na hana sha da fataucin barasa
  • A daren ranar Talata ne jami'an hukumar suka cafke motar, inda suka kama direban motar da wasu mutum biyu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wata babbar mota makare da kwalaben barasa fiye da dubu 24 da aka kwace daga hannun masu fasa kwauri da tsakar dare.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari a wani babban kanti a jihar Nasarawa, sun kashe mutum 4

Babban daraktan hukumar, Alhaji Abba Sufi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a yayin da yake duba motar da aka kwace a hanyar Zariya a daren ranar Talata.

Hisbah ta kama kwalaben giya a Kano
Hukumar Hisbah a Kano ta kama mota makare da kwalaben giya. Hoto: Hisbah Board Kano
Asali: Twitter

Yadda Hisbah ta kama mota makare da kwalaban giya

Ya yi nuni da cewa jami’an Hisbah a jihar sun zage damtse wajen aiwatar da dokar hana fasa kwaurin barasa da sauran abubuwa masu sa maye a jihar, The Punch ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Sufi:

"An kama motar dake dauke da sama da kwalabe dubu 24 na barasa daga hannun masu fasa kwauri a hanyar Zaria da tsakar dare."

Shugaban hukumar ya yabawa jami’an Hisbah bisa hadin kai da suka yi da masu ruwa da tsaki a yaki da safarar barasa a jihar, kan matsayar da jihar ta dauka na bin tsarin shari’a.

Hisbah za ta tabbatar da tsarin shari'ah a Kano

Kara karanta wannan

Manyan shari'o'i 5 da aka gagara kai karshensu a shekarar 2023

A nasa jawabin, mukaddashin kwamandan sashen kwararru kan manyan laifuka na hukumar, Fu’ad Dorayi, ya ce an kama direban motar da wasu mutum biyu.

Dorayi ya godewa jami'an rundunar na Dawakin Kudu, inda ya bukaci jama’a da su kai rahoton duk wata mota da ke dauke da kayayyakin da ake zargin na laifi ne.

Hanyoyin da masu fasa kwaurin ke amfani da su sun hada da titin Kano/Zaria, titin Kano-Gwarzo-Dayi, titin Kano-Katsina, titin Kano-Maiduguri, da titin Kano-Hadejiya.

Bidiyon yadda aka kama motar

Wani ma'abocin shafin X, mai suna Arewa guy, @Arewa_guy ya wallafa bidiyon yadda hukumar ta kama motar giyar.

Abin da ya sa turawa ke janye jiki daga yin kasuwanci a Najeriya

A wani labarin, kungiyar jam'iyyun siyasar Najeriya (CNPP), ta gargadi Shugaba Tinubu kan illolin da ke tattare da rashin saka hannun jarin turawa a kasuwancin Najeriya.

CNPP ta koka kan yadda turawan ke janye jikinsu, saboda matsalolin tsaro da suka addabi kasar, inda ta ba gwamnati shawarar abin da ya kamata ta yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.