Bidiyon katon din giya 3,600 da Hisbah ta kama an ɓoye cikin buhunan abincin kaji a Kano
- Hukumar Hisbah ta sake kama katon din giya 3,600 da aka boye cikin abincin kaji a Jihar Kano
- Wata bidiyo da ta ke yawo a dandalin sada zumunta ya nuna babban kwamandan Hisbah yana zakulo giyan daga motar
- Hukumar ta Hisbah ta jadadda cewa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin yaki da ta ke yi abubuwan da suka sabawa koyarwa addinin musulunci
Jihar Kano - Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wani babban mota makare da kiret din giya daban-daban da aka boye su cikin buhunnan abincin kaji, SaharaReporters ta ruwaito.
A cikin wani faifan bidiyo da LIB ta wallafa, an gano babban kwamandan Hisbah, Harun Ibn Sina da wasu ma'aikatan hukumar suna bude zakulo kwalaben giyan da aka boye a motar da ke dauke da abincin kaji.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
An ruwaito cewa motar ta taso ne daga Kwanar Dangora tana kan hanyar ta na zuwa garin Kiru a Jihar Kano.
Wannan na zuwa ne kwanaki biyar bayan da hukumar ta Hisbah ta kama wasu motoccin dauke da katon 5,760 na giyan a hanyar Kano zuwa Madobi.
Mai magana da yawun hukumar, Lawan Ibrahim Fagge ne ya sanar da hakan a ranar Laraba da ta gabata.
Sanarwar ta ruwaito cewa babban kwamandan hukumar yana cewa jami'an na Hisbah sun kama masu laifin ne misalin karfe 4 na safiyar ranar Laraba.
Ya ce:
"Hukumar Hisbah ta hana sayar da giya a jigar domin hana saka maye."
Ibn Sina ya kara da cewa hukumar za ta cigaba da yakin da ta ke yi ga masu safarar barasa da miyagun kwayoyi da jihar.
Ya jinjinawa jami'an hukumar, masu bada gudunmawa da masu ruwa a tsaki bisa jajircewarsu, yana mai cewa ta'amulli da kayan maye abin damuwa ne a jihar.
Kwamandan ya ce hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wurin aikin ta na tabbatar da hana ta'amulli da kayan maye a jihar.
Asali: Legit.ng