Gwamna Abba Zai Yi wa Ma’aikatan Kano Karin Kudi Saboda Cire Tallafin Man Fetur

Gwamna Abba Zai Yi wa Ma’aikatan Kano Karin Kudi Saboda Cire Tallafin Man Fetur

  • Abba Kabir Yusuf ya saurari koke-koken ma’aikata bayan Bola Ahmed Tinubu ya janye tsarin tallafin man fetur
  • Kwamitin da Gwamnatin Kano ta kafa ya bada shawarar ayi wa kowane ma’aikacin jihar karin kudi a albashi
  • Ma’aikatan gwamnatin jiha da na kananan hukumomi za su samu N20, 000, za a biya ‘yan fansho N15, 000

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kano - Gwamnatin jihar Kano za tayi wa ma’aikatanta da ‘yan fansho karin wani kaso a cikin albashinsu saboda halin da ake ciki.

Ibrahim Adam, hadimin jagoran NNPP na kasa watau Rabiu Musa Kwankwaso, ya shaida haka a shafin X (Twitter) a ranar Talata.

Gwamnatin Kano
Abba zai yi wa ma'aikatan Kano karin N20, 000 Hoto: Ibrahim Adam
Asali: Facebook

Cire tallafin man fetur a Najeriya

Gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta janye tallafin mai wanda ya jawo farashin fetur ya tashi a 2023.

Kara karanta wannan

NNPC na rikici da ‘yan kasuwa, ana zancen litar fetur ta haura N1200 a kasuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga kusan N200, wannan mataki ya jawo litar man fetur ta koma fiye da N600.

An kai wa Abba kuka a Kano

Malam Ibrahim Adam ya ce lura da halin da ake ciki, ma’aikatan gwamnati da wadanda su ka yi ritaya, sun kai kuka a Kano.

Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta duba rokon da ma’aikatan suka yi karkashin inuwar NLC da TUC a watan Oktoban shekarar 2023

Kungiyoyin ‘yan kwadago da na ‘yan kasuwa sun bukaci gwamnatin Abba Gida Gida ta kawowa al’umma saukin matsin lambar tattali.

Gwamnan Kano ya ji kukan ma'aikata

Cikin gaggawa, gwamnan ya kafa kwamitin na musamman da zai duba lamarin a Kano. Leadership ta kawo wannan labari a yau.

Jawabin ya ce a karshe dai kwamitin nan ya yanke shawarar fara biyan ma’aikata kudin tallafin N20, 000 daga Disamban 2023.

Kara karanta wannan

Kano: Babban Malami ya faɗi mafita 1 tak da ta rage wa Gwamna Abba gabanin hukuncin Kotun Koli

Wannan tallafi zai shafi ma’aikatan gwamnatin jiha da wadanda ke kananan hukumomi.

Nade-naden mukamai a Kano

A farkon makon nan ne Legit ta samu labari daga hadimin gwamnan, Salisu Hotoro cewa an rantsar da manyan sakatarorin gwamnati.

Abba Yusuf ya rantsar da sakatarori 21 tare da masu bada shawara na musamman 15 da kimanin karfe 1:00 na jiya a gidan gwamnati.

Rahoton Daily Nigerian ya ce an nada Aliyu Ibrahim Kuki a matsayin shugaban karamar hukumar Bebeji ya canji wanda ya rasu.

Bola Tinubu zai yi karin albashi?

A jawabinsa na sabuwar shekara, ana da labari duk da matsalolin da ake ciki, Bola Tinubu ya nuna da gaske yake yi wajen cin nasara.

Shugaban kasa Tinubu zai dage wajen ganin talaka ya samu sauki, zai yi wa ma’aikata karin albashi a 2024 kamar yadda ake sa rai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng