Kano: Babban Malami Ya Faɗi Mafita 1 Tak da Ta Rage Wa Gwamna Abba Gabanin Hukuncin Kotun Koli

Kano: Babban Malami Ya Faɗi Mafita 1 Tak da Ta Rage Wa Gwamna Abba Gabanin Hukuncin Kotun Koli

  • Malamin addini ya roƙi Gwamna Abba Kabir Yusu ya dage da yin addu'a kan lafiyarsa gabanin hukuncin kotun kolin Najeriya
  • Joshua Iginla, a hasashensa na abubuwan da zasu auku a 2024, ya ce ya hango kujerar Gwamna Yusuf na Kano tana tangal-tangal
  • Ya ƙara da cewa da yiwuwar a samu tashin yamutsi da kuma tada hankalin mutane a jihar duk sakamakon hukuncin kotun koli

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - An roƙi Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tashi tsaye ya dage da addu'ar kada wata rashin lafiya ta kama shi yayin da ake dakon zaman shari'ar zaben Kano a kotun koli.

Malamin addinin kirista, Joshua Iginla, na cocin Chamions Royal Assembly da ke Abuja ne ya yi wannam rokon ga Gwamna Abba a saƙon wahayinsa na sabuwar shekara.

Kara karanta wannan

Bayin Allah sama da 100 sun mutu yayin da bama-bamai suka tashi a wurin taro kusa da Masallaci

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
Zaben Kano: Sabon Hasashe Ya Nuna Abinda Zai Faru da Gwamna Abba a Kotun Koli Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Twitter

A hasashen da malamin ya bayyana ranar Litinin, 1 ga watan Janairu, 2023, ya ce Gwamnan Kano na bukatar matsawa da addu'a matuƙar yana son tsira da kujerarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa an faɗa masa cewa za a yi tashe-tashen hankula da rashin kwanciyar hankula a jihar Kano saboda zaman kotun koli mai zuwa.

Meyasa kotuna 2 suka tsige Abba?

Idan baku manta ba, kotun sauraron ƙarar zabe ta kori Abba daga kujerar gwamna yayin da ta zare haramtattun kuri'u daga cikin kuri'un NNPP a zaben 18 ga watan Maris.

Da ya ɗaukaka ƙara zuwa gaba, kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja ta kuma tsige Gwamma Abba saboda ba ɗan jam'iyar NNPP bane lokacin da ya tsaya takara.

Kotunan biyu sun ayyana Nasir Yuusf Gawuna na jam'iyyar APC a matsayin sahihin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kano.

Kara karanta wannan

Kotun koli na shirin yanke hukunci, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake motsi mai girma a jihar Kano

Me malamin ya hango zai faru a kotun koli?

Da yake tsokaci kan shari'ar gabanin zaman kotun koli a sabon hasashensa na 2024, Malamin ya ce:

"Ya kamata gwamnan ya dage addu'a kan lafiyarsa da aminci wajen kare kujerarsa, na hango tashin yamutsi da rikicin jama'a sakamakon hukunci mai zuwa."

Mun koma ga Allah - Jigon NNPP

Yayin hira da wakilin Legit Hausa, wani jigon NNPP, Sa'idu Abdullahi, ya ce babu wanda ya san mai zai faru a kotun koli sai Allah, kuma dama tuni suka rungumi addu'o'i.

Malam Sa'id ya ce dukkan ɓangarorin biyu watau APC na NNPP sun koma yin taron addu'o'in neman nasara a kotun koli saboda suna ganin komai zai iya faruwa.

Ya ce:

"Ni musulmi ne kuma na yi imani Allah ke yin komai, babu wanda ya san taƙamaiman hukuncin da kotun koli zata yanke, amma muna fatan Abba ya samu nasara."
"Mun san APC sun fi mu ƙarfi domin su ke da mulki a ƙasa to amma ba abinda ya gagari Allah, su kansu sun tsorata, sun bi hanyar da muka bi ta yin addu'o'in neman nasara."

Kara karanta wannan

"Akwai matsala" Fitaccen malamin addini ya gano makomar gwamnan PDP na arewa a kotun ƙoli

Sanata Barau ya buɗe wa wasu mutane kofofin samun arziki

A wani rahoton kuma Sanata Barau Jibrin ya raba motocin Sharon guda 60 da mazauna jihar Kano domin taimaka masu su dogara da kansu.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce wannan ba shi ne na farko kuma ba zai zama na ƙarshe ba da izinin Allah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel