"Ka Fasa Auren": Matashi Ya Shiga Damuwa Bayan Ya Gano Babban Cin Amanar da Wacce Zai Aura Ta Yi

"Ka Fasa Auren": Matashi Ya Shiga Damuwa Bayan Ya Gano Babban Cin Amanar da Wacce Zai Aura Ta Yi

  • An ɗage ɗaurin aure har zuwa wani lokaci bayan da amaryar ta ɗauki cikin wani wani mutum daban ba zato ba tsammani
  • Duk da raɗaɗin da yake ji, angon ya ba da shawarar cigaba da bikin, wanda hakan ya haifar da rikici da ƴan uwansa
  • Masu amfani da yanar gizo sun yi ta bayyana ra'ayoyinsu kan lamarin, suna ba da ra'ayoyi daban-daban kan shawarar da angon ya yanke

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Wata mata ta bayyana yadda ba zato ba tsammani aka ɗage wani ɗaurin aure bayan cin amanar da amaryar ta yi.

A cewar wata mata mai suna @HRH_onyx akan manhajar X, cikin amaryar ba na angon da za ta aura ba ne.

Kara karanta wannan

Harin Plateau: Jam'iyyar PDP ta fadi laifin Tinubu, ta gaya masa muhimmin abu 1 da ya kamata ya yi

Cin amanar budurwa ya sa an fasa daurin aura
Amarya ta dauki juna biyu wanda ba na ango ba Hoto: @himarkley, Klaus Vedfelt/ Getty Images. Hotunan an yi amfani da su kawai domin misali.
Asali: Getty Images

Cikin da amarya ta yi ya kawo cece-kuce

Wannan lamarin ya haifar da tashin hankali na rashin tabbas kuma ya haifar da tambayoyi game da makomar dangantakarsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da haka, duk da yanayin, angon yana tunanin cigaba da bikin, shawarar da ta fuskanci adawa mai ƙarfi daga danginsa.

Rashin amincewar dangin ya ƙara daɗa wani nau'i na rikitarwa ga yanayin da ya riga ya kasance mai sarƙaƙiya, inda masoyan biyu suka rasa abin yi.

Mai ba da labarin ta rubuta akan X:

"An dakatar da bikin auren da ya kamata a yi saboda matar tana da cikin wata ɗaya, kuma cikin ba daga angon da za ta aura ba ne, saboda angon ya tafi yawon shaƙatawa. Mutumin ya ce yana son cigaba da bikin. Ƴan uwansa sun ce a'a."

Wane martani masu amfani da yanar gizo suka yi?

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da jami'in dan sanda ya rasa ransa a hannun budurwarsa, an fdi abin da ya faru

Masu amfani da yanar gizo sun bayyana ra'ayoyinsu sosai kan lamarin.

@loshantii ya rubuta:

"Dalilin da ya sa yake son cigaba shi kaɗai ya sani. Ba ruwansa da soyayya. Yana da mugun nufi."

@Anigboson ya rubuta:

"Ban gane mutumin ba. Me yasa kake son ɗaukar nauyin ciki wanda ba naka ba? Ƴan uwansa su tsaya tsayin daka. Mu, surukai na X, muna goyon bayansu sosai."

@Mareeyah_ ta rubuta:

"Wataƙila yana so ya cigaba da hukunta ta. Wasu mazan haka suke."

@IamEkene_ ya rubuta:

"Mutumin ya duba duk abin da ya kashe kuma baya son ya yi asara, shi ne kawai dalilin da ya sa yake son komai ya cigaba, ko kuma yana sonta sosai kuma bai damu ba, me na sani?"

Amarya Ta Soke Bikinta

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata amarya ta soke bikin aurenta da angonta ana saura sati ɗaya biki.

Amaryar dai ta soke bikin auren ne saboda angonta ya ce ba shi da kuɗin da zai biya domin ɗaukar nauyin raƙashewa a bikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel