Jerin Sunayen Jami’o’i 20 da Suka Fi Kowane Kyau a Nahiyar Afrika a Shekarar 2023

Jerin Sunayen Jami’o’i 20 da Suka Fi Kowane Kyau a Nahiyar Afrika a Shekarar 2023

Africa - Jama’a suna tambaya game da makarantun jami’o’in da su ka fi kyau musamman a Najeriya da sauran kasashen Afrika.

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Wasu jami'o'i su ka fi kyau a 2023?

Wani bincike na Statisense da aka fitar a karshen Disamban 2023 ya nuna jami’o’in da su ka yi fice a Afrika, an bar Najeriya a baya sosai.

Jami'o'i
Jami'o'in Afrika mafi kyau a 2023 Hoto: ukzn.ac.za, techcabal.com, www.expedia.com
Asali: UGC

Ficen jami'o'in Afrika ta Kudu da Masar

Mafi yawan jami’o’in da ake ji da su a yau a Afrika na kasashen Afrika ta Kudu da Masar ne.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jerin da aka wallafa a shafin X da aka fi sani da Twitter, akwai jami’o’i irinsu Al-Azhar wanda ta na cikin mafi dadewa a tarihin duniya.

Kara karanta wannan

Yanzu aka fara: Miyagu sun yi alkawarin sake kai hari bayan kashe mutum 195 a Filato

Jami’ar Kafr El Sheikh da aka bude a shekarar 2006 a Masar ce wanda aka cike da ita.

Ina labarin jami'o'in Najeriya?

Jami’o’i biyu – Covenant da jami’ar Ibadan da ke jihohin Ogun da Oyo ne su ka iya fitar da Najeriya daga kunya a shekarar nan ta 2023.

Covenant jami’a ce da fitaccen faston nan, David Oyedapo ya gina shekaru 20 da su ka wuce, makarantar tana nan ne a garin Otta a Ogun.

Baya ga jami’ar Covenant wanda ta kiristoci ce, akwai jami’ar Ibadan wanda gwamnatin tarayya ta kafa tun shekarar 1948 a Ibadan.

A jerin, ba a maganar jami’o’i irinsu Ahmadu Bello ta Zariya, jami’ar Nsukka, jami’ar Bayero da ke Kano da manyan jami’o’in da ke Legas.

Ya jami'o'in duniya suke samun daraja?

Akwai abubuwan da ake dubawa wajen darajanta jami’a a duniya, daga ciki akwai yadda daliban kasashen waje su ke zuwa karatu cikinta.

Kara karanta wannan

Tsohuwar Jakadar Najeriya Ta Shigar da Karar Ministan Buhari a Kotu a Kasar Waje

Baya ga farin jini, masana sun ce ana duba yanayin daliban da aka yaye, saurin samun aikin tsofaffin dalibai da takardun da aka wallafa.

Jami'o'i 20 da suka fi kyau a 2023

1. Jami’ar Cape Town

2. Jami’ar Stellenbosch

3. Jami’ar Witwatersrand

4. Jami’ar Johannesburg

5. Jami’ar KwaZulu-Natal

6. Jami’ar KwaZulu-Natal

7. Jami’ar Cape Coast

8. Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Masar da Jafan

9. Jami’ar North-West

10. Jami’ar Western Cape Verde

11. Jami’ar Alexandria

12. Jami’ar Al-Azhar

13. Jami’ar Amurka ta Masar

14. Jami’ar Aswan

15. Jami’ar Masar

16. Jami’ar Covenant

17. Jami’ar Damietta

18. Jami’ar Free State

19. Jami’ar Ibadan

20. Jami’ar Kafr El Sheikh

Za a sha wahala a 2024 a Najeriya

Ana da rahoto cewa masana tattalin arziki sun ce akwai karancin kaya da rashin tsaro da za su jawo karin wahalar rayuwa a 2024.

Dr. Abubakar Sani Abdullahi ya ce cire tallafin fetur ya sa manoma ba su zuwa ganokin da ke nesa ba, hakan zai jawo karancin abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel