2023: Muhimman Abubuwa 10 da Suka Faru a Majalisar Tarayya a Shekarar Da Ta Wuce
FCT, Abuja - Abubuwa da yawa sun faru a shekarar da ta gabata watau 2023, ba a bar majalisar tarayyar Najeriya a baya ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Daily Trust ta yi dogon nazari, ta jero manya-manyan abubuwan da su ka faru a bara a majalisar da aka kaddamar a watan Yuni.
1. Sababbin shiga
Bayan zaben 2023, an zubar da mafi yawan ‘yan majalisar tarayya – hakan ya bada dama kusan 70% na wadanda su ka zo, su ka zama sababbin shiga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Neman shugabanci
Takara tsakanin Abdulaziz Yari da Godswill Akpabio tayi zafi a majalisar dattawa, amma a majalisar wakilai, Tajuddeen Abbas ya samu gagarumar nasara.
3. Katobarar Godswill Akpabio
A lokacin da za a tafi hutu a watan Agusta, an ji Godswill Akpabio yana cewa an turawa Sanatoci kudin huta, hakan ya fusata abokan aikinsa a majalisa.
4. Rade-radin tsige shugaban majalisa
Akwai lokacin da jita-jita ta rika yawo cewa za a tunbuke Akpabio. Daga baya ta bayyana kujerar tsohon gwamnan na jihar Akwa Ibom tana nan daram.
5. Kwan-kwon kasafin kudi
Bayan Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da kundin kasafin kudin 2024, sai aka ji wani ‘dan majalisa yana cewa babu komai tattare da kwalayen da aka kawo.
6. Shari’ar zabe
Kotun daukaka kara ta tsige ‘yan majalisa; Elisha Abbo, Simon Davou Mwadkwon, Napoleon Bali, Abubakar Sadiku Ohere da Darlington Nwokocha.
Hukuncin kotu ya yi waje da akalla mutane 15 a majalisar wakilai a shekarar bara.
7. Badakalar daukar aiki
‘Yan majalisar wakilan tarayya sun yi zargin ana tafka badakala ta IPPIS wajen daukar ayyukan gwamnati. Hakan ya jawo bincike a hukumar FCC.
8. Shugaban marasa rinjaye
Jaridar ta kawo rigimar da aka yi a kan wanda zai zama sabon shugaban marasa rinjaye a cikin abubuwan da su ka faru a majalisar tarayya a 2023.
9. Sayen motoci
Maganar motocin da aka saya domin ‘yan majalisa da sanatoci ta bar baya da kura. Majalisar Najeriya ta cigaba da kashe biliyoyi a kan manyan motoci.
10. Kasafin kudi
Kafin shekarar 2023 ta kare, sai da aka ji ‘yan majalisar tarayya sun kara N147bn a a kasafin kudinsu, ma’ana za su kashe fiye da N300bn a shekarar nan.
Kasafin kudin Majalisa a 2024
Ana da labari kusan abubuwa 30 ne 'yan majalisa da sanatoci za su kashe kudinsu a kai a shekarar 2024 da aka shiga wanda za su ci kusan N350bn.
Kusan N170bn za a kashe a ofisoshin ‘yan majalisa, hadiman ‘yan siyasan za su lakume N20bn, kuma majalisa za ta gina wurin ajiye motocin N6bn.
Asali: Legit.ng