An Sallami Wasu ’Yan N-Power, Ba Su Daga Cikin Wadanda Za a Biya Bashin Albashin Watanni 9

An Sallami Wasu ’Yan N-Power, Ba Su Daga Cikin Wadanda Za a Biya Bashin Albashin Watanni 9

  • Zubin farko (Batch A) na rusasshen shirin N-Power na gwamnatin jam’iyyar APC ya fara ne a watan Satumban 2016 kuma ya kare bayan shekaru hudu
  • Zubi na biyu (Batch B) sun ci gajiyar shirin da ya tallafawa talakawa da yawa ne a tsakanin Agustan 2018 da Yuli 2020 kamar yadda aka bayyana
  • Masu sai iuma zubi na uku da hudu (Batch C1 da C2) da aka dauka a cikin shekarar 2021, kuma su ne a yanzu ake kokarin sallama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim kwararren editan fasaha, kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas.

FCT, Abuja - N-Power ta ce masu cin gajiyar shirin a zubin farko da na biyu (Batch A da B) ba sa cikin shirin a halin yanzu.

Kara karanta wannan

Zargin rashawa: Atoni Janar na Kano Dederi ya shiga matsala, an nemi a hukunta shi

Sai dai, har yanzu masu kula da shirin a gwamnatin Tinubu sun yi shuru game da makomai wadanda aka dauka a karkashin zubi na uku da hudu (Batch C1 da C2).

An dakatar da 'yan N-Power
An sallami rukunin 'yan N-Power | Hoto: Npower, Fed Min of Humanitarian Affairs, Disaster Management and Social Development
Asali: Facebook

Yadda aka kawo karshen ‘Batch A da B’

Wani mai amfani da shafin sada zumunta na X ne ya dago bayani game da shurun da gwamnatin tarayya ta yi game da makomar wasu ‘yan N-Power da ke karskashin shirin farko da na biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A martanin N-Power, tuni ai gwamnati ta salami diban farko da na biyu, don haka ba sa cikin wadanda ke cikin shirin a yanzu.

A martanin N-Power:

“Don Allah ku sani cewa, Batch A da B a yanzu ba sa cikin shirin.”

An rike kudin ‘yan N-Power

Ya zuwa yanzu, ‘yan Najeriya da yawa na ci gaba da jira da sa ran gwamnatin tarayya za ta sallame su komai kankantarsa.

Kara karanta wannan

Jami’an Tsaro sun cika ko ina, NNPP da APC sun hakura da zanga zanga a Kano

A baya-bayan nan dai gwamnatin tarayya ta yi alkawarin biyan ‘yan N-Power kudaden da suke binta na shirin na tsawon watanni tara.

Ya zuwa yanzu dai ba a biya ba, kuma suna ci gaba da sa ran watarana za a biya su duk da har yanzu babu wasu bayanai game da biyan.

Koken matasa game da rike kudadensu

An bukaci masu cin gajiyar N-Power da su ke bin bashi su kara hakuri kan basukansu, Legit ta tattaro.

Wadanda ke bin bashin mafi yawanci 'yan rukunin 'C' ne da aka dauka a shekarar 2021 inda wasu ke bin bashi har na tsawon watanni tara.

A cikin wata sanarwa da N-Power su a fitar a shafin Twitter, sun sha alwashin kawo karshen dukkan matsalolin da ake fuskanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.