Bayan Shafe Shekaru 7 a Kulle, an Sake Bude Masallacin Juma’a da Gwamnan PDP Ya Shiga Lamarin
- A karshe, Gwamna Dauda Lawal ya shiga lamarin rikicin da ya jawo rufe masallacin Juma'a har tsawon shekaru bakwai
- Matsalar da aka samu a masallacin garin Moriki da ke karamar hukumar Zurmi shi ya yi sanadin rufe masallacin
- Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a yau Asabar 30 ga watan Disamba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Zamfara - Gwamna Dauda Lawal Dare ya tsoma baki kan rikicin akida a wani masallacin Juma'a na Izala a jihar Zamfara.
Matsalar da aka samu a masallacin garin Moriki da ke karamar hukumar Zurmi ya yi sanadin rufe masallacin na tsawon shekaru bakwai.
Wane mataki Dauda Lawal ya dauka?
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar a yau Asabar 30 ga watan Disamba, cewar Premium Times.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Idris ya ce daukar matakin da gwamnan ya yi ya zama dole don tabbatar da kawo daidaito a tsakaninsu.
Dauda Lawal ya ce zaman lafiya shi ke kawo fahimtar juna da kuma inganta rayuwar jama'a a kasa musamman a wannan lokaci.
Wane yarjejeniya aka yi kan rikicin masallacin?
Sanarwar ta ce:
"A jiya gwamnatin jihar Zamfara karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal Dare ta sasanta rikicin akida da aka shafe shekaru bakwai ana yi.
"Gwamnatin ta fahimci daukar matakin ya zama dole kan dakile rikicin a babban masallacin Juma'a da ke Moriki a karamar hukumar Zurmi.
"Gwamnatin ta dauki matakai da za su dakile rikicin don samar da zaman lafiya a tsakanin al'umma."
Gwamna Dauda Lawal ya umarci ma'aikatar harkokin addinai da ta gina sabon masallaci ga dayan bangaren, Leadership ta tattaro.
Ana sa ran sabon masallacin za a kammala shi a cikin watanni uku kacal yayin da dukkan bangarorin su ka amince da hakan.
Rikici ya sanya rufe masallacin Juma'a shekaru 7
A wani labarin, an shiga kotu bayan rikicin bangare ya barke a tsakanin kungiyar Izala da ke garin Moriki a karamar hukumar Zurmi.
An samu sabani tsakanin kungiyar Izalar da ke Jos da kuma bangaren Kaduna kan shugabancin masallacin.
Asali: Legit.ng