Rashin tsaro: Yanzu makiyaya da manoma duk sun mallaki AK-47, Lalong

Rashin tsaro: Yanzu makiyaya da manoma duk sun mallaki AK-47, Lalong

- Simon Lalong, gwamnan jihar Plateau ya koka kan yadda bindigu da sauran makamai ke bazuwa cikin al'umma wanda ya ce ba alheri bane

- Lalong, wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin arewa ya ce bincike a Plateau ya nuna manoma da makiyaya duk suna mallakar AK-47

- Lalong ya yi kira ga gwamnati ta aiwatar da dokar sauya tsarin kiwo ya zama na zamani don kawo karshen rikicin makiyaya da manoma

Gwamna Plateau, Simon Lalong, a ranar Talata, ya koka kan yadda makamai ke bazuwa a tsakanin jama'a ciki har da AK - 47 tsakanin makiyaya da manoma a kasar, The Punch ta ruwaito.

Lalong, wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin Arewa, ya jaddada bukatar aiwatar da dokar kasa ta sauya tsarin yadda ake kiwo domin kawo karshen rikici tsakanin makiyaya da manoma.

DUBA WANNAN: Nan ba da daɗewa ba Boko Haram za su iya haɗewa da ƴan bindiga, Sheikh Gumi

Rashin tsaro: Makiyaya da manoma duk yawo suke da AK-47, Lalong
Rashin tsaro: Makiyaya da manoma duk yawo suke da AK-47, Lalong. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

Ya yi wannan jawabin ne a hirar da aka yi da shi a shirin 'Sunrise Daily' a gidan talabijin na Channels Television da The Punch ta bibiya.

Gwamnan ya ce ya zama dole a haramta kiwo a fili sannan a rungumi tsarin ruga ko kiwo a kebeben wuri domin samun zaman lafiya a kasar.

DUBA WANNAN: Mun sha duka da yunwa: Fasinjojin da ƴan bindiga suka sace a Neja sun magantu

Ya ce, "A yau, muna ganin matsalar da kyale mutane kiwo a ko ina ya haifar. Amma suma (makiyayan) suna neman mafita; idan ka musu bayani, suma suna son zama a wuri daya, za su so su dena yawo da AK-47. Ba kare wadanda ke daukan AK-47 na ke yi ba amma kada ka manta a binciken mu, mun gano cewa ba makiyaya Fulani kadai ke yawo da AK-47 ba, manoma ma suna yawo da AK-47.

"Makamai na yaduwa a cikin al'umma saboda yunkurin kare kai. Kowa na son ya kare kansa, bai dace mu bari hakan na faruwa ba.

"A lokacin da aka samu rikici tsakanin makiyaya da manoma a Plateau, mun kama mutane, makiyaya da manoma duk suna dauke da AK-47. Amma idan baka son dukkansu su rika yawo da AK-47, ya zama dole ka dakile shigowar makamai sannan ka koyar da su sabbin dabarun noma na zamani."

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel