Hukuma ta ceto yaro dan-mari da iyayensa suka daure wata uku

Hukuma ta ceto yaro dan-mari da iyayensa suka daure wata uku

- Yan Sanda sun kubutar da wani karamin yaro wanda kakar shi ta daure har na tsawon wata uku

- ‘Yan sandan jihar Ogun sunyi nasarar ceto wani yaro dan shekara 12, mai suna Segun Azeez, wanda kakarshi mai suna Mrs. Yemi Kazeem ta daure shi har na tsawon wata uku

Hukuma ta ceto yaro dan-mari da iyayensa suka daure wata uku
Hukuma ta ceto yaro dan-mari da iyayensa suka daure wata uku

Kwamishinan ‘yan sandar jihar, Ahmed Iliyasu, ya jagoranci tawagar ‘yan sandan zuwa gidan da abin ya auku a garin Ife-Lagba, a karamar hukumar Ewekoro, domin kubutar da yaron, sannan kuma su kama kakar tasa. 

Mahaifiyar yaron, Yomi Kazeem, wadda ma’aikaciyar lafiya ce, sun rabu da mahaifin yaron, itace ta bada sarka da mukullin da aka yi amfani dasu aka kulle yaron. A cewar uwar da kakar, sunyi hakan ne saboda su hana yaron guduwa. 

Segun wanda ya dinga zubar da hawaye bayan an kubutar dashi, yace sun samu wani dan rikici a gidan mahaifin sa dake Sagamu, inda yake zargin wani yayi mashi asiri, abinda ya razana shi kenan har ya tilasta shi ya gudu daga gidan. 

DUBA WANNAN: Babu alakar Tinubu da Obasanjo kan wasikar sa

Ya kara da cewa yasha wahala da kuma yunwa, abinda ya tilasta shi ya dakatar da Karatun sa a Sagamu. Ya ce lokacin da mahaifiyar shi ta dauko shi daga Sagamu zuwa Obada, yayi tunanin cewar wahalar shi ta kare kenan, ashe abin ba haka yake ba. 

Yayin da kwamishinan ‘yan sandan yake magana da manema labarai ya bayyana cewar abin da ya faru da Segun din a matsayin rashin imani, wanda zai iya yin sanadiyyar yaron ya rasa ranshi. Ya bayyana cewar sun gano laifin ne ta hanyar masu binciken fasaha wato (FSARS), inda suka gano yaron a cikin mawuyacin hali, a wurin da aka daure shi din. 

Kakar yaron, Yemi Kazeem, ta shaida wa ‘yan jarida cewar yaron baya jin magana, sannan ta daure shine don hana shi satar kayan mutane da kuma guduwa daga gidan. Tace tana zargin yaron yana da aljanu, inda ta dinga yi masa addu’a akan Allah ya bashi sauki. 

Mahaifiyar yaron tace, ita bata dauki abinda suka yi wa yaron a matsayin laifi ba, tace sun daure shine saboda, ko zasu samu su huta da maganar da yake jawo musu

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng