Dalilin da yasa matsalar garkuwa da mutane ya ki ci ya ki cinyewa - 'Yan sanda
- Kakakin rundunar 'yan sanda, DCP Frank Mba ya bayyana dalilan da yasa har yanzu an gaza shawo kan matsalar garkuwa da mutane a Najeriya
- Kakakin 'yan sandan ya ce akwai matsaloli da ke adabar al'umma da suka hada da rashin ayyukan yi, matsanancin talauci, shan miyagun kwayoyi da sauransu
- Frank Mba ya kuma bayar da shawarwarin hanyoyin da za a bi domin magance matsalar ta garkuwa da mutane a Najeriya
Kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya, DCP Frank Mba ya yi fashin baki a kan wasu dalilan da ke janyo aikata laifin garkuwa da mutane ko sace mutane da kuma hanyoyin da za a bi domin shawo kan matasalar cikin wata hira da ya yi da Daily Trust.
Da aka masa tambaya kan dalilin da yasa matsalar ta garkuwa da mutane ta ki ci ta ki cinyewa duk da irin kokarin da rundunar 'yan sanda da sauran jami'an tsaro ke yi.
DCP Frank Mba ya ce: "Garkuwa da mutane sun kasu kashi daban-daban a Najeriya. Akwai garkuwa da mutane da ake yi saboda samun dama, akwai wadanda suke sace mutane sakamakon karyan lagwan 'yan tayar da kayan baya na Neja Delta, akwai sace mutane da ake yi sakamakon ta'addanci a arewacin Najeriya da kuma yin garkuwa da mutane a matsayin hanya da kungiyoyin ta'adda keyi domin samun kudi.
DUBA WANNAN: Mai a daidaita sahu ya kashe abokin aikinsa a Kano
"Akwai dalilai dama da ke sanya ingiza al'umma aikata garkuwa da mutane, wasu daga ciki sun hada da rashin ayyukan yi, yawaitar talauci a kasa, shan miyagun kwayoyi, bazuwar makamai cikin al'umma, rashin bawa 'yan sanda da sauran jam'an tsaro isasun kayan aiki, tsatsauran ra'ayi, bangar siyasa, tabarbarewar tarbiya a gidaje da sauransu."
Hanyoyin da za a bi domin magance wannan matsalar a cewar DCP Mba sun hada da: "Kaddamar da shirin samar da aiki da dimbin matasa a kasar misali a harkar wasanni da motsa jiki, harkar noma, kasuwanci da dama wa da matasa a gwamnati musamman a matakin kananan hukumomi.
"Akwai kuma bukatar samar da sabbin kayan yaki da ta'adanci na zamani da kuma hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro ta yadda za su rika musayar bayyanan sirri da kuma kara kiyaye iyakar kasar mu domin hana shigo da haramtattun makamai, safarar mutane da sauransu."
Kazalika, Mba ya ce cikin masu garkuwa da mutane 261 da aka kama a Najeriya, 131 cikinsu an kama su ne cikin watanni uku bayan kaddamar da atisayen 'Operation Puff Adder'.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng